Abba Ya Fitar da 'Yan Takarar APC da za Su Kalubalanci Kwankwaso a Zabe

Abba Ya Fitar da 'Yan Takarar APC da za Su Kalubalanci Kwankwaso a Zabe

  • Bayan sauya sheka, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zaɓi ’yan takarar APC domin cike gurbin kujerun ’yan majalisar jiha biyu da suka rasu a Kano
  • Rahotanni sun nuna cewa Hon Alhajiji PA Kankarofi zai tsaya takara a KMC, yayin da Hon Musayyib Kawu Ungogo zai fafata a mazabar Ungogo
  • Hakan na zuwa ne bayan Rabiu Kwankwaso ya tsayar da ’ya’yan marigayan ’yan majalisar domin tsayawa takara a zaɓen cike gurbin da za a yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Abba Kabir Yusuf ya sanar da ’yan takarar da za su fafata a zaɓen cike gurbi na kujerun Majalisar Dokokin Jihar Kano biyu bayan rasuwar ’yan majalisar da ke wakiltar KMC da Ungogo.

Wannan mataki ya biyo bayan komawar Gwamna Abba Kabir Yusuf jam’iyyar APC, inda ya fara daukar matakai na siyasa a sabon matsayinsa a cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Sai Tinubu: 'Dan Atiku ya sha alwashi, za a hadu da shi a kada mahaifinsa a 2027

Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso
Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Kwankwaso a wani taro. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Hadimin gwamna Abba Kabir, Salisu Yahaya Hotoro ne ya wallafa sunayen 'yan takarar APC a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Zaɓen cike gurbin na zuwa ne bayan mutuwar Hon Aminu Ungogo da Hon Sarki Aliyu Daneji, waɗanda suka rasu a watan Disamba, 2025.

'Yan takarar APC da Abba ya fitar

Jam’iyyar APC a Kano ta fitar da Hon Alhajiji PA Kankarofi a matsayin ɗan takararta domin cike gurbin kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar KMC.

Haka kuma, an rahoto cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da Hon Musayyib Kawu Ungogo domin tsayawa takara a mazabar Ungogo.

Majiyoyi sun bayyana cewa wannan shi ne mataki na farko da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka a fagen siyasa bayan sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Haka kuma, wannan ne karo na farko da gwamnan zai shiga sahun jagororin APC wajen fuskantar zaɓe a Kano, lamarin da ke nuni da sabon salo a siyasar jihar.

Kara karanta wannan

An fara siyasa: Barau ya sauya sunan kungiyarsa bayan Abba Kabir ya koma APC

'Yan takarar APC a majalisar jihar Kano
Wadanda Abba Kabir ya zaba su yi takara a APC a majalisar Kano. Hoto: Salisu Yahaya Hotoro
Source: Facebook

'Yan majalisar Kano da suka rasu

Rahotanni sun bayyana cewa zaɓen cike gurbin ya zama dole ne bayan rasuwar ’yan majalisar jihar biyu a watan Disamba, 2025.

Marigayi Hon Aminu Ungogo, wanda shi ne shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar, ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya a harabar Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Premium Times ta rahoto cewa Aminu Ungogo ya rasu ne jim kadan bayan sanar da rasuwar dan majalisar mai wakiltar KMC, Hon. Sarki Aliyu.

Wadanda Kwankwaso ya ba takara a NNPP

A gefe guda kuma, jam’iyyar NNPP ta sanar da amincewa da Aminu Sa’ad da Nabil Daneji, ’ya’yan marigayan ’yan majalisar, domin tsayawa takara a kujerun da iyayensu suka bari.

Shugaban jam’iyyar NNPP a Kano, Hashim Dungurawa, ya bayyana cewa an cimma wannan matsaya ne bayan shawarwari da jagoran jam’iyyar na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, da sauran masu ruwa da tsaki suka jagoranta.

Kara karanta wannan

Shugaban hukumar alhazai ya hakura da gwamnatin Abba, ya yi murabus

Dungurawa ya ce manufar wannan tsari ita ce tallafa wa iyalan marigayan ’yan majalisar tare da tabbatar da ci gaba da wakilcin al’ummar mazabun KMC da Ungogo.

Barau ya yi wa Abba gata a APC

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya yi kira ga mutanensa da su marawa gwamna Abba Kabir Yusuf baya da ya koma APC.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya nuna amincewa da sauya sunan kungiyar da ke tallata shi tare da shugaba Bola Tinubu.

Sunan Abba Kabir Yusuf ya samu shiga sunan kungiyar Barau, inda ya ce zai mara wa gwamnan baya domin samun nasara a jihar Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng