Abin da Kwankwaso da Mutanen Kano Suka Dauki Hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC

Abin da Kwankwaso da Mutanen Kano Suka Dauki Hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso da NNPP sun dauki sauya shekar Gwamnan Kano zuwa APC a matsayin cin amana
  • Mai magana da yawun NNPP na kasa, Ladipo Johnson ne ya bayyana hakan, ya ce abin da Abba Kabir Yusuf ya yi cin amnar jama'ar Kano ne
  • Ya bayyana yadda al'umma suka zabi jam'iyyar NNPP a zaben shekarar 2023 duk da ba ta da wani kafaffen tsari ko wata kujera ko guda daya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Jam’iyyar NNPP ta kara nuna tsananin bacin ranta kan sauya shekar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.

NNPP ta bayyana cewa tsohon dan takararta na shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya dauki lamarin matsayin cin amana.

Gwamna Abba da Kwankwaso.
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Sanusi Bature
Source: Facebook

Kakakin jam’iyyar na kasa, Ladipo Johnson, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake jawabi a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Jita jita ta kare, 'yan majalisa 22 sun sauya sheka daga NNPP zuwa APC a Kano

Bacin ran Rabiu Kwankwaso da mutanen Kano

Da aka tambaye shi ko Sanata Kwankwaso yana jin an yaudare shi, Johnson ya ce wannan cin amana ya wuce kan jagoran jam’iyyar kawai, har ma da al’ummar jihar Kano baki daya.

Ya ce:

"A gaskiya, shi [Kwankwaso] yana ji a ransa cewa an ci amanarsa. Amma batun ya wuce kansa kadai har da mutanen Kano.
"Jama'a sun jure shekaru takwas na abin da suka kira mummunan mulki, suka fito kwansu da kwarkwata suka ba jam’iyyar NNPP amanarsu ta hanyar jagorancin Kwankwaso, amma ka duba abin da aka masu yanzu."

Yadda mutanen Kano suka ba Abba amana

Johnson ya tunatar cewa jam’iyyar NNPP ba ta da wani tsari na siyasa a jihar Kano kafin zaben 2023, amma duk da haka ta samu nasara, kamar yadda Vanguard.

"Sun zabi NNPP ne daga zuciyarsu. Ba mu da kujerar ko da kansila balle ciyaman, amma muka ci jihar Kano. Jama'a sun tsaya wa Abba Kabir Yusuf tun daga kotun zabe, zuwa kotun daukaka kara har zuwa kotun koli.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito; An ji dalilin da ya ja hankalin Gwamna Abba zuwa APC

“Kwatsam ba tare da tuntubar mutane ba, ka mayar da mulki ga wadanda mutane suka ki zabarsu bayan shekaru takwas. Wannan aikin cin amana ne,” in ji shi.
Barau da Gwamna Abba.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin da Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Abba zai ci zabe ko ba Kwankwaso?

Dangane da ikirarin cewa Abba Kabir Yusuf zai iya zama gwamna koda ba tare da goyon bayan Kwankwaso ba, Johnson ya yi watsi da wannan maganar.

“Yana da saukin a fadi haka yanzu saboda sun ga gwamnati ta koma tsaginsu, amma ina da tabbacin Mai Girma Abba Kabir Yusuf ba zai iya tsayawa a ko’ina a duniya ya fadi hakan ba,” in ji shi.

Da yiwuwar a tsige Mataimakin gwamnan Kano

A wani rahoton, kun ji cewa sauya shekar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ta jefa mataimakinsa, Aminu Gwarzo cikin rashin tabbas kuma kujerarsa ta fara tangal-tangal.

Rahoto ya nuna cewa an taso Mataimakin gwamnan Kano duba da yadda har yanzu ya ki fita daga NNPP kuma ya jaddada mubaya'arsa ga Kwankwaso.

Wasu majiyoyi sun ce an fara duba yiwuwar sanya Majalisar dokokin Kano ta tsige Kwamared Aminu Gwarzo daga matsayin Mataimakin gwamnan Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262