Babbar Magana: Gwamna Abba Na Shiga APC, Ganduje Ya Fadi Jagoran Jam'iyyar a Kano
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya koma APC mai mulki a Najeriya a hukumance a ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tarbi Mai girma Abba Kabir Yusuf tare da yi masa albishir kan zaben 2027
- Ganduje ya bayyana cewa dukkanin masu neman takara a APC sun amince su marawa Gwamna Abba baya domin ya yi tazarce
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ba Gwamna Abba Kabir Yusuf tabbaci kan zaben 2027.
Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, cewa zai yi nasara a zaben gwamna na shekarar 2027.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Ganduje ya bayar da wannan tabbaci ne a Kano yayin da yake tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya koma jam’iyyar APC a ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026.
Me Ganduje ya ce kan shigowar Abba APC?
Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana dawowar Gwamna Abba zuwa APC a matsayin abin tarihi kuma mai alfanu ga jam’iyyar da kuma jihar Kano baki ɗaya.
Ya bayyana cewa jam’iyyar za ta mara masa baya gaba ɗaya domin ya sake samun wa’adi na biyu.
“Za ka yi nasara a wa’adi na biyu a 2027. Mun tattauna da duk masu neman takara kuma duk sun amince za su mara maka baya."
- Abdullahi Umar Ganduje
Ganduje ya yi farin cikin dawowar Gwamna Abba
Ya bayyana cewa dawowar Abba Kabir Yusuf jam’iyyar a matsayin dawowa gida, inda ya tuna cewa gwamnan na daga cikin waɗanda suka kafa APC tun farko, kafin daga bisani ya bar jam’iyyar sakamakon bambancin ra’ayin siyasa.
“Wannan rana ce mai cike da tarihi da abin tunawa. Mai girma Gwamna, muna maraba da kai wajen dawowa gida APC. Lokacin da aka kafa jam’iyyar, kana tare da mu, amma daga baya sabanin siyasa da fahimtar juna suka sa ka bar ta. Yanzu ka dawo."
- Abdullahi Umar Ganduje
Ganduje ya yabi Gwamna Abba
Tsohon gwamnan Kano ya bayyana Gwamna Abba Yusuf a matsayin ɗan siyasa mai tafarkin ci gaba, yana mai cewa salon jagorancinsa da dabi’unsa sun yi daidai da akidar jam’iyyar APC.
“Mun san ka a matsayin ɗan siyasa mai ra’ayin ci gaba ta fuskar fahimtarka, kalamanka da dabi’arka."
- Abdullahi Umar Ganduje
Wanene jagoran APC a jihar Kano?
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa bisa al’adar jam’iyyar APC, Gwamna Abba Kabir Yusuf zai zama jagoran jam’iyyar a jihar Kano kai tsaye.
“A APC, dukkan gwamnonin da ke kan mulki su ne jagororin jam’iyyar a jihohinsu. Don haka kai ne jagoran APC a jihar Kano."
- Abdullahi Umar Ganduje

Source: Facebook
Ganduje ya kuma tabbatar wa gwamnan cewa za a yi masa adalci a cikin jam’iyyar, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa APC za ta samu gagarumar nasara a zabubbuka masu zuwa.
“Yayin da kake shigowa jam’iyyar, muna tabbatar maka cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ma zai yi nasara a zaben 2027. APC za ta tsaya tsayin daka tare da kai."
- Abdullahi Umar Ganduje
'Dan Kwankwaso ya yi murabus daga gwamnatin Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamishinan matasa da raya wasanni na jihar Kano, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ya yi murabus daga kan mukaminsa.
Dan na jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne da zuciya mai nauyi.
Hakazalika, ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi na yi wa al’ummar jihar Kano hidima.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


