Kurunkus: Dalilin 'Yan Majalisar Kano 22 na Komawa APC daga NNPP
- 'Yan majalisar dokokin jihar Kano guda 22 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki bayan ficewa daga NNPP
- Daga cikin masu sauya shekar zuwa a APC a ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026 har da shugaban majalisar, Alhaji Jibril Falgore
- 'Yan majalisar sun yi bayani dalla-dalla kan dalilin da ya sanya suka yanke shawarar rabuwa da jam'iyyar NNPP wadda suka lashe zabe karkashinta a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - ’Yan majalisar dokokin jihar Kano 22 sun sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki.
’Yan majalisar da suka sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC sun hada da shugaban majalisar, Alhaji Jibril Falgore.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce an sanar da sauya sheƙar tasu ne a yayin zaman majalisa na ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026 a Kano.
Meyasa 'yan majalisar Kano suka koma APC?
Yan majalisar sun bayyana cewa bukatar samar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jihar ne ya sa suka ɗauki wannan mataki.
Sauya shekar 'yan majalisar ya gudana ne yayin zaman majalisar wanda Alhaji Jibril Falgore ya jagoranta.
Da yake magana bayan zaman, shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini, ya ce an yanke shawarar ne baki ɗaya bayan tattaunawa mai zurfi.
A cewarsa, an ɗauki matakin ne bisa la’akari da muradun al’ummar jihar gaba ɗaya.
Amfanin sauya sheka zuwa APC
Ya ce sauya shekar na da nufin rage rikicin siyasa da karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali, musamman duba da kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta a halin yanzu.
Lawan Hussaini ya bayyana cewa daidaita jihar da jam’iyyar da ke mulki a matakin tarayya zai bai wa Kano damar samun kulawa da goyon bayan gwamnatin tarayya kamar yadda sauran jihohi ke amfana.
Ya kara da cewa kara haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya abu ne mai muhimmanci domin tunkarar matsalolin tsaro da sauran kalubalen da ke addabar jihar.
Majalisar dokokin Kano ta tattauna wasu batutuwa
Dan majalisar ya kuma bayyana cewa an tattauna wasu harkokin majalisa a zaman, ciki har da gabatar da kudirin dokar da ke neman gyara dokar hukumar ayyukan majalisar dokokin jihar Kano.
Shugaban masu rinjayen ya ce gyaran da ake shirin yi na da nufin karfafa majalisar dokoki tare da inganta ayyukanta.

Source: Facebook
’Yan majalisar sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da tabbatar da haɗin kai, zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci a jihar.
Sun ce sauya shekar ba ta samo asali daga muradin kashin kai ba, sai dai daga kudirin bai ɗaya na tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaban jihar Kano.
Sun kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu tare da mara baya ga duk wani yunkuri da zai karfafa zaman lafiya da ci gaba a faɗin jihar Kano.
Abin da ya ja hankalin Gwamna Abba zuwa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar kula da allunan tallace-tallace ta jihar Kano, Kabiru Dakata, ya kare Gwamna Abba Kabir kan shirin komawa APC.
Kabiru Dakata ya karyata rade-radin da ke cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bar jam’iyyar NNPP ne saboda burin kansa na siyasa.
Shugaban na hukumar KASA ya ce shirin gwamnan na komawa jam’iyyar APC na da nufin daidaita jihar Kano da gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng


