Zance Ya Fito, An Ji Matakin da Za a Dauka kan Mataimakin Gwamnan Kano idan Ya Ki Komawa APC

Zance Ya Fito, An Ji Matakin da Za a Dauka kan Mataimakin Gwamnan Kano idan Ya Ki Komawa APC

  • Har yanzu dai ba a ji matsayar mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo game da batun sauya sheka ba
  • Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an fara duba matakin da ya dace a dauka kansa idan har ya zabi ci gaba da zama a jam'iyyar NNPP
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam'iyyar NNPP a ranar Juma'a, 23 ga watan Janairu, 2026

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP da komawarsa APC ya jefa mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo, cikin matsin lamba na siyasa.

Rahoto ya nuna cewa an taso mataimakin Gwamnan Kano duba da yadda har yanzu ya ki fita daga NNPP kuma ya jaddada mubaya'arsa ga jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Jita jita ta kare, 'yan majalisa 22 sun sauya sheka daga NNPP zuwa APC a Kano

Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo Hoto: @AminuGwarzo
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an fara duba yiwuwar sanya Majalisar dokokin Kano ta tsige Kwamared Aminu Gwarzo daga matsayin Mataimakin gwamnan Kano idan ya ci gaba da zama a NNPP.

Gwamna Abba ya gigita siyasar Kano

Tun farko dai matakin Gwamna Abba na raba gari da NNPP, wanda ya sanar a ranar Juma’a, 23 ga watan Janairu, 2025, ya girgiza fagen siyasar jihar Kano.

Sai dai 'yan majalisar dokokin jiha 22, mambobin majalisar wakilai takwas da shugabannin kananan hukumomi 44 duk sun bi sahunsa.

Mafi yawan 'yan majalisar zartarwa (Kwamishinoni) ta Kano sun riga sun bi gwamnan, ban da tsirarun wasu da suka ajiye mukamansu.

Wane mataki ake shirin dauka?

Wani hadimin Abba ya shaida wa Jaridar Guardian cewa ana nazarin shirin yin amfani da 'yan majalisar da ke goyon bayan gwamna domin tsige mataimakin gwamnan idan ya ki yin murabus da kansa.

Majiyar ta bayyana cewa, tun farko akwai wani shiri na boye da aka so a tsige Abba domin a mayar da mataimakinsa matsayin gwamna lokacin da maganar sauya sheka ta fara fitowa.

Kara karanta wannan

Ana batun sauya shekar Gwamna, jagora a APC ya dawo NNPP Kwankwasiyya

Gwamna Abba.
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: @AbbaKYusuf
Source: Twitter

Sai dai shirin ya ruguje ne bayan jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso ya gano cewa mafi yawan 'yan majalisar da ake sa ran za su yi aikin sun riga sun koma bangaren gwamna Abba.

Da yiwuwar a tsige Aminu Gwarzo

A halin yanzu, dabarar da bangaren Gwamna Abba ke shirin amfani da ita ce umartar wadannan mambobin majalisa su tsige Aminu Gwarzo, ganin yadda ya kekashe kasa kan lallai shi yana tare da Kwankwaso.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kokarin jin ta bakin mai magana da yawun gwamna da na mataimakinsa ya ci tura.

Gwamna Abba ya koma jam'iyyar APC

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf , ya koma jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya a hukumance a ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026.

Gwamna Abba, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, ya sanar da hakan ne a wani gagarumin taro da aka shirya a babban dakin taron da ke gidan gwamnatin Kano.

Tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje da Mataimakin shugaban Majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin sun halarci taron tarbar Abba Kabir Yusuf.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262