Abu Ya Girma: APC Ta Yi Magana kan Sauya Shettima a Zaben 2027

Abu Ya Girma: APC Ta Yi Magana kan Sauya Shettima a Zaben 2027

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi tsokaci kan batun da ke yawo na shirin sauya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a zaben 2027
  • APC ta fito ta yi gamsashshen bayani kan jita-jitar sauya Kashim Shettima wadda ta sake yaduwa a cikin 'yam kwanakin
  • Mai magana da yawun bakin APC na kasa, Felix Morka, ya bayyana abin da jam'iyyar ta sanya a gaba a wannan lokacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta yi magana kan rade-radin da ake yi na sauya Kashim Shettima a zaben 2027.

Jam'iyyar APC ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ana shirin sauya Kashim Shettima daga matsayin mataimakin shugaban kasa a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaben 2027.

APC ta ce ba gaskiya ba ne batun sauya Kashim Shettima
Kashim Shettima na jawabi a wajen taron FEC Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka, ya fitar a shafin X a.ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Shettima: 'Babban kuskuren da Tinubu da APC za su tafka a zaben 2027'

Me APC ta ce kan sauya Kashim Shettima?

Felix Morka ya bayyana rahotannin a matsayin hasashe kawai, tsabagen karya kuma wadanda ba su da tushe kwata-kwata.

Jam’iyyar ta ce rade-radin sun kara kamari ne bayan da aka fara yaɗa sunayen wasu mutane da ake hasashen za su maye gurbin mataimakin shugaban kasar.

“Jam’iyyarmu na bayyanawa a fili cewa waɗannan labarai hasashe ne kawai, karya ne kuma babu ba su da wani tushe a kansu."

- Felix Morka

APC ta bukaci a daina yada jita-jita

APC ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su guji faɗaɗa irin waɗannan jita-jita da ta bayyana a matsayin labarai daga majiyoyi masu son tayar da fitina kuma marasa tabbas.

Felix Morka ya ce irin waɗannan rahotanni an ƙirƙire su ne domin haddasa rikici da ruɗani a harkokin siyasar kasa.

Jam’iyyar mai mulki ta jaddada cewa har yanzu dokar hana gudanar da harkokin siyasa tana nan daram bisa dokoki da ka’idojin zaɓe da ke aiki.

Kara karanta wannan

Ganduje ya dura Najeriya, zai je taro Gwamna Abba zuwa APC a Kano

Me APC ta sanya a gaba?

Felix Morka ya ce jam’iyyar ta maida hankali ne kan goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima domin aiwatar da ajandar “Renewed Hope” ta gwamnatin tarayya.

“A wannan lokaci, jam’iyyarmu ta maida hankali ne kan tallafa wa Shugaba Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima wajen aiwatar da ajandar 'Renewed Hope' ta gwamnatin tarayya."

- Felix Morka

APC ta musanta batun sauya Shettima
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

APC ta ce sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa suna sauya fasalin tattalin arziki a hankali, suna samar da wadata tare da inganta rayuwar al’umma.

Jam’iyyar ta kuma gargadi ministoci, manyan jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyya da kada su rika hura wutar hasashe marasa amfani.

Ta bukace su da su maida hankali kan hidima ta gaskiya da kuma karfafa nasarar gwamnatin Tinubu.

Shettima: APC za ta yi kuskure a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a APC ya ja kunnen jam'iyyar kan sauya Kashim Shettima a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Hannatu Musawa ta yi gargadi kan ajiye Kashim Shettima a 2027

Farfesa Haruna Yerima ya bayyana cewa jam'iyyar APC za ta tafka babban kuskure idan ta sauya Kashim Shettima daga matsayin abokin takarar Mai girma Bola Tinubu.

Ya bayyana cewa wadanda ke kira da a sauya tsarin tikitin su ne mutanen da suka yi adawa karara da tikitin Tinubu/Shettima a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng