'Dan Kwankwaso Ya Yi Murabus daga Mukamin Kwamishina a Gwamnatin Abba
- 'Dan jagoran Kwankwasiyya, Mustapha Rabiu Kwankwaso ya ajiye muƙaminsa na Kwamishinan Matasa da Wasanni na Kano
- Mustapha Rabi'u Musa Kwankwaso ya ajiye mukaminsa ne a ranar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke koma wa APC a hukumace
- Ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana fatan matasa da wasanni za su ci gaba da samun kulawa a gwamnatinsa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Mustapha Rabiu Kwankwaso ya sanar da yin murabus daga muƙaminsa na Kwamishinan Matasa da Raya Wasanni na Jihar Kano.
Wannan na zuwa ne a lokacin da siyasar Kano ta dauki zafi bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rabu da mahaifinsa, ya sauya sheka zuwa APC.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da ya rattaba hannu da kansa, ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne da zuciya mai nauyi.
Mustapha Kwankwaso ya bar gwamnatin Abba
Mustapha Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana godiyarsa ga gwamnan bisa damar da ya ba shi na yi wa al’ummar jihar hidima.
Mustapha Rabi'u Musa Kwankwaso ya kara da cewa:
“Ina miƙa matuƙar godiyata ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba ni na yi wa al’ummar Jihar Kano hidima."
Ya bayyana cewa a tsawon lokacin da ya shafe a ofis, ya koyi muhimman darussa da ƙwarewa, waɗanda ya ce za su ci gaba da kasancewa tare da shi ko bayan ya bar gwamnati.
Duk da Mustapha Rabi'u Kwankwaso bai fayyace takamaiman dalilin da ya sa ya ajiye muƙamin ba, watakila ba zai rasa nasaba da yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bar mahainfinsa a NNPP zuwa APC ba.
Sakon Mustapha Kwankwaso ga gwamnatin Kabo
Dangane da makomar ɓangaren da yake jagoranta, Kwankwaso ya bayyana fatan cewa matasan Jihar Kano za su ci gaba da samun kulawa da goyon bayan da ya dace daga gwamnati.
Haka kuma, ya nuna ƙwarin gwiwar cewa shirye-shiryen bunƙasa wasanni a jihar za su ci gaba da habaka domin amfanin matasan jihar.

Source: Facebook
Ya ce:
“Yayin da nake yin murabus, ina addu’ar cewa matasan Jihar Kano za su ci gaba da samun kulawa da goyon bayan da suka dace."
Ya kuma yi fatan alheri ga Gwamna da gwamnatin Kano, tare da bayyana fatan za a ci gaba da aiki domin amfanin Kanawa.
Hadimin Abba ya bar jam'iyyar NNPP
A wani labarin, kun ji cewa babban mai ɗauko rahoto a Hukumar Lantarki ta Karkara (REB), Muktar Abdullahi Asad, ya sanar da janyewarsa daga harkokin siyasar jam’iyya.
Muktar Asad ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce matakin ya biyo bayan ficewar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyar NNPP.
A cewarsa, ya yanke shawarar nesanta kansa daga fafutukar jam’iyya domin mayar da hankali kan siyasar da ta ginu a kan nagartar hali, gaskiya da karamcin mutum.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

