Abba Ya Sa Hotunan Ganduje a Gidan Gwamnatin Kano, an Cire na Kwankwaso
- An hango sauyin hotunan manyan 'yan siyasa a gidan gwamnatin Kano, inda bayan cire hoton Rabiu Musa Kwankwaso aka sanya na Abdullahi Ganduje
- Sauyin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen karbar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC bayan ficewarsa daga NNPP
- Rahotanni sun nuna sama da ‘yan majalisa 20 da kwamishinoni sun bi gwamnan zuwa APC, yayin da wasu suka tsaya a NNPP tare da Rabiu Musa Kwankwaso
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – An fara hango alamun sauyin siyasa a fadar Gwamnatin Kano bayan da aka saka hotunan tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, da wasu manyan jiga-jigan APC a dakin taro na gidan gwamnatin jihar.
Sauyin ya biyo bayan rashin ganin hotunan jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da sauran jiga-jigan jam’iyyar NNPP daga wurin, a daidai lokacin da ake shirin ayyana komawar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC.

Source: Facebook
Rahotannin da Premier Radio ya wallafa a Facebook daga gidan gwamnatin sun nuna cewa shirye-shiryen sun yi nisa domin tarbar gwamnan zuwa APC.
Hotunan Ganduje a gidan gwamnatin Kano
A cewar bayanan da aka samu, an hango hotunan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Kano, tare da na tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, da Murtala Sule Garo.
Haka kuma, an ga hotunan wasu jiga-jigan APC da suka fafata da Rabiu Musa Kwankwaso a zaben shekarun 2019 da 2023, duk kuwa da cewa a wancan lokaci ana yakin neman zaben Abba Kabir Yusuf ne karkashin inuwar jam’iyyar NNPP.
Baya ga haka, an kuma hango hoton Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, wanda shi ma babban jigo ne a APC, a cikin gidan gwamnatin Kano.
Sai dai a daya bangaren, ba a hango hoton Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba ko wani fitaccen jigo na jam’iyyar NNPP a cikin dakin taron, abin da ya kara tabbatar da canjin yanayin siyasar da ke gudana a jihar.

Source: Facebook
Shirye-shiryen karbar Abba Kabir a APC
Sauyin hotunan na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran manyan ‘yan siyasa ciki har da Abdullahi Ganduje da sauran jiga-jigan APC za su halarci taron karbar Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan majalisar dokokin jihar Kano sama da 20, tare da wasu kwamishinoni, sun riga sun bi gwamnan wajen komawa APC.
Sai dai duk da haka, wasu kwamishinoni da masu rike da mukamai a gwamnatin jihar sun zabi ci gaba da zama a jam’iyyar NNPP tare da jagoranta, Rabiu Musa Kwankwaso.
Tun da fari, mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a Facebook cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai koma jam’iyyar APC a yau Litinin, 26, Janairu, 2026.
Maganar Keyamo kan Rabiu Kwankwaso
A wani labarin, mun kawo muku cewa Ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Festus Keyamo ya yi magana kan siyasar jihar Kano.
Keyamo ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso ya samu kan shi a tsaka mai wuya bayan fitar Abba Kabir Yusuf da manyan 'yan siyasa daga NNPP.
Duk da haka, ministan ya bayyana cewa Kwankwaso na da zabin haduwa da PDP, LP ko APC yana mai cewa da wahala ya shiga ADC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


