Shettima: 'Babban Kuskuren da Tinubu da APC Za Su Tafka a Zaben 2027'

Shettima: 'Babban Kuskuren da Tinubu da APC Za Su Tafka a Zaben 2027'

  • Jigo a jam'iyyar APC, Farfesa Haruna Yerima, ya yi tsokaci kan batun sauya tikitin Tinubu/Shettima a zaben 2027
  • Farfesa Haruna Yerima ya bayyana cewa mutanen da ke son a sauya Shettima na daga cikin wadanda ke adawa da Muslim-Muslim tun a 2023
  • 'Dan siyasar ya bayyana cewa wadanda ke wannan kiran ba su da tunani mai kyau kuma suna da karancin gogewa a siyasa

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Farfesa Haruna Yerima, ya yi magana kan batun sauya Kashim Shettima a zaben 2027.

Farfesa Haruna Yerima ya gargadi jam’iyyar APC da kada ta kuskura ta sauya tikitin takarar shugaban kasa na Tinubu/Shettima gabanin zaben shekarar 2027.

An gano kuskuren da APC da Tinubu za su yi a zaben 2027
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima Hoto: @DOlusegun, @Stanleynkwocha
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Lahadi, 25 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Hannatu Musawa ta yi gargadi kan ajiye Kashim Shettima a 2027

Batun sauya Kashim Shettima a 2027

Farfesa Haruna Yerima ya ce wadanda ke kira da a sauya tsarin tikitin su ne mutanen da suka yi adawa karara da tikitin Tinubu/Shettima a zaben 2023.

“Babu shakka, sauya tikitin takarar shugaban kasa na Tinubu/Shettima ba zai haifar wa APC alheri ba a zaben shekarar 2027."
“Abin takaici ne ganin cewa mutanen da ba su taba yarda tikitin Tinubu/Shettima zai kai ga nasara a 2023 ba, su ne yanzu ke aiki dare da rana domin sauya shi."
"Ya kamata a dakatar da su tun yanzu, idan ba haka ba jam’iyya mai mulki za ta fuskanci mummunan kaye a 2027.”

- Farfesa Haruna Yerima

Jigo a APC ya soki masu son a sauya Shettima

Haruna Yerima ya ce masu neman a canza tikitin Tinubu/Shettima ta hanyar tilasta dauko Kirista daga shiyyoyin Arewa ta Tsakiya ko Arewa maso Yamma ba wai kawai gajeran tunani suke da shi ba, har ma da karancin iya siyasa.

Kara karanta wannan

Tsofaffin 'yan majalisa sun yi watsi da mara wa Tinubu baya a zaben 2027

Ya ce an wadatar da shiyyar Arewa ta Tsakiya ta hanyar ba ta manyan mukamai a gwamnatin tarayya, jaridar leadership ta kawo rahoton.

“Shiyyoyin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma da ke fafutukar neman tikitin Mataimakin shugaban kasa a 2027, sun riga sun amfana da manyan mukamai da suka hada da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Ministan tsaro, shugaban jam’iyyar APC na kasa."
"Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Shugaban kamfanin NNPCL, babban hafsan sojojin lasa (COAS), da sauransu."

- Farfesa Haruna Yerima

An bukaci kada a sauya Kashim Shettima a 2027
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a cikin ofis Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

Shettima ya samu shaida mai kyau

Haruna Yerima ya ce Sanata Kashim Shettima ya nuna cikakkiyar biyayya da jajircewa ga Shugaba Bola Tinubu.

“Akwai bayanai a fili da ke nuna cewa Sanata Kashim Shettima ya kasance mataimaki mai biyayya kuma jajirtacce ga Shugaba Tinubu. Ba ya hayaniya."
"Hatta masu adawa da shi a siyasa ba za su musanta cewa jajirtaccen haziki ne mai karfin tunani ba. Tarihinsa a siyasa abin koyi ne."

- Farfesa Haruna Yerima

Dogara ya magantu kan maye gurbin Shettima

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya yi magana kan batun maye gurbin Kashim Shettima a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Yayin da ake hasashen sauya Shettima, an ce Tinubu na shirin sauya shi da Gwamna

Yakubu Dogara, ya ce bai kamata a fara sanya shi a rade-radin neman mataimakin takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba.

Ya jaddada cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne kadai ke da ikon yanke hukuncin abin da ya fi dacewa ga jam’iyyar APC da kasa baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng