Jita Jita Ta Kare, 'Yan Majalisa 22 Sun Sauya Sheka daga NNPP zuwa APC a Kano
- 'Yan Majalisar dokokin jihar Kano 22 sun sanar da ficewarsu daga NNPP zuwa APC mai mulki a hukumance yau Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026
- Mambobin Majalisar sun sanar da hakan ne a zamansu na yau Litinin, wanda ya gudana karkashin jagorancin Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore
- Hakan na zuwa ne yayin da ake dakon sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya tsara zama cikakken 'dan APC a yau Litinin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - A rahoton da muka samu yanzu haka, mambobi 22 na majalisar dokokin jihar Kano sun sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulkin kasar nan a hukumance.
'Yan majalisar sun sanar da sauya shekar tasu ne a ranar Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026, kwanaki kadan bayan Gwamna Abba Akabir Yusuf ya yi murabus daga jam'iyyar NNPP.

Source: Facebook
Yadda Gwamnan Kano ya fice daga NNPP
The Cable ta ruwaito cewa Gwamna Abba ya fice daga jam'iyyar NNPP ne kwanaki kadan bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A cikin wata wasika da ya aika wa shugaban NNPP na mazabar Diso-Chiranchi da ke karamar hukumar Gwale a Kano, gwamnan ya bayyana "rikicin cikin gida" da takaddama kan shugabanci a matsayin manyan dalilan ficewarsa.
Gwamna Abba ya bar NNPP ne tare da mafi yawan mambobin majalisar dokokin jihar, mambobin majalisar wakilai ta tarayya takwas, da kuma dukkan shugabannin kananan hukumomi 44 na Kano
Jerin wadanda suka koma APC a Majalisa
A bidiyon zamansu na yau Litinin da Radio Kano ya wallafa a Facebook, 'yan Majalisar dokokin Kano da ke tare da Abba Gida-Gida, sun sanar da komawa APC a hukumance.
Daga cikin wadanda suka koma APC akwai kakakin majalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore (Rogo) da mataimakinsa, Hon. Muhammad Bello Butu Butu (Tofa/Rimin Gado).
Sauran sun kunshi shugaban masu rinjaye, Hon. Lawan Hussain (Dala), mataimakinsa, Hon. Garba Shehu Fammar da babban mai tsawatarwa, Hon. Muddasir Ibrahim Zawachiki (Kumbotso).

Source: Facebook
Sai kuma Zakariyya Abdullahi Nuhu (Gabasawa), Lawal Tini (Ajingi), Musa Tahir Haruna (Albasu), Ali Lawan Alhassan (Bagwai/Shanono), Ali Muhammad Tiga (Bebeji), Hafiz Gambo (Bunkure), da Rabiu Shuaibu (Dawakin Kudu).
Kazalika, akwai Tukur Mohammed (Fagge), Murtala Muhammad Kadage (Garko), Abdulmajid Isah Umar (Gwale), Engr. Ahmad Ibrahim (Karaye), Alhassan Zakari (Kura/Garun Malam), da Suleiman Mukhtar Ishaq (Madobi).
Sauran su ne Abdulhamid Abdul (Minjibir), Muhammad Ibrahim (Rano), Kabiru Sule Dahiru (Tarauni), da Ali Abdullahi Manager (Wudil).
APC ta yi maraba da Gwamna Abba
A wani rahoton, kun ji cewa APC ta yi maraba da sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da ware masa kati mai lamba 001 a rijistar mambobin jam'iyya na jihar Kano.
Sakataren jam'iyyar APC na jihar Kano, Ibrahim Zakari Sarina, ne ya bayyana hakan yayin da yake magana da manema labarai.
Ya bayyana shigowar gwamnan a matsayin abin da ya kara wa APC karfi, yana mai cewa Abba zai tahi ne tare da adadi mai yawa na zababbun jami’an gwamnati da masu rike da mukaman siyasa a Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

