An Kawata Gidan Gwamnatin Kano da Tutocin Jam'iyyar APC, Hotuna Sun Bayyana

An Kawata Gidan Gwamnatin Kano da Tutocin Jam'iyyar APC, Hotuna Sun Bayyana

  • An kawata fadar gwamnatin jihar Kano da sababbin tutocin jam'iyyar APC yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shirya komawa APC yau
  • Rahotanni sun nuna cewa zuwa safiyar yau Litinin, 2026, an cire duk wata tuta ta NNPP a gidan gwamnatin tare da maye gurbin da ta APC
  • Gwamna Abba Gida Gida ya shirya tsaf domin komawa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya bayan tsawon lokacin ana yada jita-jita

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gidan gwamnatin jihar Kano ya dauki sabon kamanni, inda aka kawata shi da tutocin APC, a daidai lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke shirin komawa jam’iyyar a hukumance.

Rahotanni sun nuna cewa tuni aka sauke duk wasu tutocin jam'iyyar NNPP tare da maye gurbinsu da na APC a fadar gwamnatin da ke cikin birnin Kano.

Kara karanta wannan

Abba ya sa hotunan Ganduje a gidan gwamnatin Kano, an cire na Kwankwaso

Gidan gwamnatin Kano.
Tutocin jam'iyyar APC da na Najeriya da aka kafa a kofar gidan gwamnatin Kano Hoto: @AOLMarkazy
Source: Twitter

An kafa tutocin APC a gidan gwamnatin Kano

Yayin da wakilin jaridar Daily Trust ya kai ziyara harabar gidan gwamnatin da ke Kano, ya tabbatar da cewa an sauke tutocin jam’iyyar NNPP.

Wannan sauyi ya faru ne gabanin taron karbar Gwamna Abba da mukarrabansa, wanda za a gudanar a fadar ta gwamnatin Kano yau Litinin.

Bayanai sun nuna cewa tun daga kofar shiga gidan gwamnatin har zuwa cikin ofisoshi, duk an maye gurbin tutocin NNPP da na APC, inda launukan jam’iyyar suka karade ko’ina a cikin ginin.

Wannan sauyi ya kara tabbatar da jiran da ake yi na dawowar gwamnan zuwa jam’iyyar APC, a daidai lokacin da ake samu gagarumin sauyin fasalin siyasa a jihar Kano.

Gwamna Abba ya shirya koma wa APC

Ana sa ran dai Gwamna Abba da mambobin Majalisar dokokin jihar Kano 22 da shugabannin kananan hukumomi 44 za su koma APC a hukumance yau Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Jita jita ta kare, 'yan majalisa 22 sun sauya sheka daga NNPP zuwa APC a Kano

An bayyana sauya shekar Gwamna Abba zuwa APC a matsayin komawa gida kasancewar ya tana zama a jam'iyyar a shekarar 2014.

Abba ya fara shiga APC ne a 2014, inda ya lashe zaben fitar gwani na takarar sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, matsayin da daga baya ya janye wa ubangidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Gwamna Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatinsa Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Sai dai a yanzu, Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida zai koma APC bayan shawarwari da masu ruwa da tsaki na jihar Kano

Wannan ya sa aka cire suka titocin NNPP daga fadar gwamnatin Kano, tare da maye gurbinsu da na jam'iyyar da Gwamna Abba zai koma watau APC, cewar Leadership.

'Yan majalisar Kano 22 sun koma APC

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan Majalisar dokokin jihar Kano 22 sun sanar da ficewarsu daga NNPP zuwa APC mai mulki a hukumance ranar Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanarda ficewarsadaga jam'iyyar NNPP saboda rikicin cikin gida da ya addabe ta.

Kakakin Majalisar dokokin Kano, Rt. Hon. Jibril Isma'il Falgore ne ya jagoranci yan Majalisar zuwa APC a hukumance a zamansu na yau Litinin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262