Abin Boye Ya Fito; An Ji Dalilin da Ya Ja Hankalin Gwamna Abba zuwa APC
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC bayan ficewa daga NNPP a makon da ya wuce
- Shugaban hukumar kula da allunan tallace-tallace ta Kano, Kabiru Dakata, ya kare Gwamna Abba kan shirinsa na komawa APC
- Kabiru Dakata ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a jita-jitar da ake yadawa cewa Gwamna Abba ya bar NNPP ne saboda burin kansa na siyasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Shugaban hukumar kula da allunan tallace-tallace ta jihar Kano (KASA), Kabiru Dakata, ya yi magana kan shirin sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC.
Kabiru Dakata ya karyata rade-radin da ke cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bar jam’iyyar NNPP ne saboda burin kansa na siyasa.

Source: Facebook
Shugaban na hukumar KASA ya bayyana hakan ne a shirin 'The Morning Brief' na tashar Channels Tv a ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026.
Meyasa Gwamna Abba zai koma APC?
Kabiru Dakata ya ce shirin gwamnan na komawa jam’iyyar APC na da nufin daidaita jihar Kano da gwamnatin tarayya.
A cewarsa, jihohin da APC ke mulki na samun alfanu da dama daga gwamnatin tarayya idan aka kwatanta da jihohin da ke karkashin jam’iyyun adawa.
Ya ce sauya shekar Gwamna Abba zai jawo samun karin kudade da tallafi daga gwamnatin tarayya.
“Jihohi makwabta da ke karkashin jam’iyyar APC suna cin gajiyar gwamnati a Abuja fiye da jihar Kano, kuma ban ga laifi ba idan gwamnatin tarayya ta fi fifita jihohin da ke karkashin jam’iyya daya wato APC. Don haka ba abin zargi ba ne."
"Wata dama ce ga jam’iyyar ta kara yin abin da ya dace a jihar da take mulki.”
- Kabiru Dakata
An kare Gwamna Abba kan komawa APC
Da yake ci gaba da magana kan matakin gwamnan na sauya sheka, Kabiru Dakata ya ce:
“Idan jagoran siyasa ya yi amanna cewa zai iya yin aiki mafi kyau a wata jam'iyya ta siyasa, ina ganin ya kamata a karfafa masa gwiwa ya dauki wannan mataki. Don haka batun ba wai son zuciyarsa ba ne.”
Kano ta fara cin gajiyar gwamnatin tarayya
Kabiru Dakata ya kuma bayyana cewa wani muhimmin aikin raya kasa a jihar da ya tsaya cak sakamakon karancin kudi ya samu tallafin kudi bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya daidaita jihar da gwamnatin tarayya.
“Dukkanin gwamnoni uku da suka gabata sun yi iya bakin kokarinsu, Mai girma Mallam Ibrahim Shekarau, Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje duk sun yi iya bakin kokarinsu."
"Lokacin da Mai girma Abba Kabir Yusuf ya zo, ya aiwatar da wani bangare na aikin tare da kammala wani bangare."
“Saboda wannan hadewa, gwamnatin tarayya ta amince da bayar da sama da Naira biliyan 46 domin aikin, wato aikin Wuju-Wuju."
- Kabiru Dakata

Source: Facebook
Ya jaddada cewa lamarin ba ya da alaka da muradin kashin kai, yana mai cewa duk jagoran siyasa da ya yi amanna cewa zai iya yin aiki mafi kyau a wata jam'iyya, ya dace a karfafa masa gwiwa ya dauki irin wannan mataki.
Gwamna Abba ya shirya koma wa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shirya komawa jam'iyyar APC bayan ficewa daga NNPP.
Mai magana da yawun bakin gwamnan Kano, Sanusi Bature ya ce Gwamna Abba ya shirya tsaf domin komawa jam’iyyar APC a ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026, biyo bayan ficewa daga NNPP.
Sanusi Bature ya ce yanayin tafiyar da mulki na yanzu, bukatar hadin kan kasa, da ci gaba sun sanya ya zama dole Abba Gida-Gida ya koma APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


