Dogara: Kiristan da aka Ce zai Maye Shettima a 2027 Ya Fito Ya Yi Magana
- Tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya yi magana kan rade-radin cewa zai maye gurbin mataimakin shugaban kasa a zaben 2027 a APC
- Dogara ya ce ya kamata batutuwan rabon madafun iko da daidaiton addini su ta’allaka kan adalci da gaskiya, ba tsoro ko matsin lambar siyasa ba
- Ya bayyana cewa ana tattaunawa kan yiwuwar canza mataimakin shugaban kasa, amma duk shawarar da aka dauka dole ta kasance mai hada kan ‘yan kasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya ce bai kamata a tsoma a da rade-radin neman mataimakin takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba.
Ya yi magana yana mai jaddada cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne kadai ke da ikon yanke hukuncin abin da ya fi dacewa ga jam’iyyar APC da kasa baki daya.

Source: Facebook
Dogara ya bayyana hakan ne a shirin tashar Channels Television, a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa ana iya sauya Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, kafin babban zaben 2027.
Maganar Dogara kan sauya Shettima
Da aka tambaye shi kan rade-radin da ke danganta sunansa da yiwuwar zama abokin takarar shugaba Bola Tinubu, Dogara ya ce:
“Ku cire ni daga wannan batu, amma bari in fadi wani abu.”
Ya cigaba da cewa:
“Duk abin da muke yi bai kamata ya kasance saboda tsoron wani ko matsin lamba ba, sai dai saboda mun yarda cewa shi ne abin da ya dace.”
Dogara, wanda Kirista ne daga Arewa, ya jaddada cewa ya kamata shugabanci ya kasance mai hadin kai da adalci, domin gina kasa da kowa zai ji yana da muhimmanci a cikinta.
Batun daidaiton addini da karba-karba
Tsohon shugaban majalisar ya ce bai kamata tattaunawar karba-karbar shugabanci ta tsaya kan yankuna kadai ba, har ma ya hada da la’akari da addini.

Kara karanta wannan
Juyin mulki: Sojoji sun mika rahoto kan jami'ai 16 da ake zargi ga shugaba Tinubu
The Cable ta rahoto ya ce:
“Idan muna magana kan karba-karbar shugabanci, babu abin da zai hana mu fadada tattaunawar zuwa batun addini, domin ba batun Kiristocin Arewa kawai ba ne, batun Kiristoci gaba daya ne.”
Dogara ya kara da cewa idan aka zabi Musulmi, ko daga Arewa ko Kudu, yana wakiltar Musulmi ne gaba daya, haka nan Kirista ma duk inda ya fito yana wakiltar Kiristoci ne.
Matsayar Dogara kan sauya Shettima
Yakubu Dogara ya bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar tsayar da Kirista a matsayin abokin takarar Tinubu a 2027.
Ya ce:
“Tattaunawa ce, kuma na san cewa ana yin irin wannan tattaunawa a halin yanzu.”
Sai dai ya jaddada cewa a karshe Shugaba Tinubu ne zai yanke hukunci, yana mai cewa babu wani shugaban kasa mai ci da ya taba faduwa a zaben fitar da gwani na jam’iyyarsa.

Source: Twitter
An gargadi APC kan sauya Shettima
A wani rahoton, kun ji cewa Ministar al'adu ta kasa, Hannatu Musa Musawa ta yi magana kan rade-radin sauya Kashim Shettima a 2027.
Ministar ta bayyana cewa jam'iyyar APC mai mulki za ta fuskanci kalubale idan ta sauya Kashim Shettima da wani mataimaki a zabe mai zuwa.
Hakan na zuwa ne yayin da 'yan siyasa da masu sharhi ke magana kan yiwuwar sauke Shettima da dauko wani Kirista daga Arewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

