Ganduje Ya Dura Najeriya, Zai Je Taro Gwamna Abba zuwa APC a Kano

Ganduje Ya Dura Najeriya, Zai Je Taro Gwamna Abba zuwa APC a Kano

  • Tsohon Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya dawo Najeriya daga Birtaniya a daidai lokacin da siyasar Kano ta dauki zafi
  • Ya dawo gida a lokacin da ake sa ran Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sanar da komawarsa APC a hukumance yau Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026
  • Tuni shiri ya yi nisa inda aka kawata gidan gwamnatin Kano da tutar APC a madadin na NNPP da ke bangarori daban-daban na fadar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo Najeriya daga ƙasar Birtaniya a yau Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Ana batun sauya shekar Gwamna, jagora a APC ya dawo NNPP Kwankwasiyya

Lamarin ya zo a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulki ke shirin karɓar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bayan ya fice daga jam’iyyar NNPP a makon da ya gabata.

Ganduje ya dawo kasar nan don tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf
Tsohon Shugaban APC Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa wannan dawowa ta Ganduje ta ƙara ɗaukar hankalin masu bibiyar siyasa, ganin yadda lamuran jam’iyyu ke sauyawa a Kano cikin gaggawa.

Sauya sheka: Ganduje ya dawo Najeriya

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ana kallon wannan mataki a matsayin wani muhimmin juyi a siyasar jihar, musamman duba da irin tasirin da Ganduje ke da shi a APC.

Wata sanarwa da Kwamared Muhammad Garba, shugaban ma’aikatan Abdullahi Ganduje, ya fitar, ta nuna cewa tsohon gwamnan Kano zai kasance cikin manyan jagororin da za su halarci bikin karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ganduje ya dawo daga Birtaniya inda ya halarci zaman
Tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Twitter

Sanarwar ta bayyana cewa Ganduje na da muhimmiyar rawa wajen haɗa kai da daidaita sahu a jam’iyyar, musamman a wannan lokaci mai cike da sauye-sauye.

Ganduje ya tafi Birtaniya ne domin halartar bikin kammala karatun digiri na biyu na ‘yarsa, Fatima Ganduje, a jami’ar King’s College da ke birnin London.

Kara karanta wannan

Abin da Kwankwaso ya fada wa magoya baya bayan ficewar Abba daga NNPP

Dalilan gwamnan Kano na koma wa APC

A gefe guda kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin bayyana matsayinsa a hukumance zuwa APC.

A jiya Lahadi, Sanusi Bature, mai magana da yawun Gwamnan, ya tabbatar da cewa gwamnan zai sanar da komawarsa APC a yau Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana rikice-rikicen cikin gida a NNPP da kuma bukatar fifita ci gaban al’ummar Kano a matsayin manyan dalilan da suka sa ya yanke shawarar barin jam’iyyar da ta kai shi ga nasara a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

"Ba za a ci amana da ni ba:" Kwankwaso ya ajiye mukaminsa a gwamnatin Abba

Wannan mataki ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin magoya baya da shugabannin siyasa, musamman ganin yadda ya raba gari da jagoran NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso

Gwamnatin Kano ta yi wa Kwankwaso gugar zana

A baya, kun ji cewa Gwamnatin Kano mayar da martani kan rade-radin siyasa da suka biyo bayan rarrabuwar ra’ayi tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Sanarwar ta fito ne domin fayyace matsayar gwamnati tare da kare mutuncin gwamnan, musamman dangane da kalaman da ke yawo cewa alfarmar Kwankwaso kawai Gwamna ke ci.

A cewar gwamnatin Kano, irin wadannan kalamai ba su dace ba, domin suna rage kimar tsarin siyasa da kuma fahimtar al’ummar jihar Kano da tarihinta mai cike da sauye-sauye da jarumta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng