Abba: Gwamnatin Kano Ta Yi wa Kwankwaso Guzar Zana kan Tasiri a Siyasa
- Gwamnatin Kano ta kare ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar NNPP tare da kawo aya da hadisi domin nuna karfin tawakkali ga hukuncin Allah SWT
- Sanarwar ta jaddada cewa kiran da ake yi na cewa Abba ba zai zarce wa’adi ba tare da Rabiu Musa Kwankwaso ba, kuskure ne da ke raina tarihin siyasar Kano
- Gwamnatin ta bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da shari’o’in da ke gaban kotu sun raunana NNPP, lamarin da ya sa aka dauki matakin cikin kyakkyawar niyya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da wata sanarwa ta musamman inda ta kare matsayar Gwamna Abba Kabir Yusuf dangane da rade-radin siyasa bayan rarrabuwar ra’ayi tsakaninsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Gwamnatin ta ce cewa Abba zai fadi ba tare da Kwankwaso ba kuskure ne, domin hakan watsi ne da tsarin siyasa da tarihin Kano.

Source: Twitter
Sanarwar da Kwamishinan yada labarai Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a Facebook ta yi tsokaci kan kalaman Buba Galadima da ke cewa Abba ba zai iya samun wa’adi na biyu ba tare da Kwankwaso ba.
An yi wa Kwankwaso gugar zana
A cewar sanarwar, babu shakka Rabiu Musa Kwankwaso jigo ne a siyasar Kano, mai kwarewa da tasiri, amma hakan ba yana nufin makomar siyasar jihar na rataye a wuyan mutum guda ba ne.
Sanarwar ta kara da cewa siyasar Kano tana da nata yanayi, tarihi da wayewar kai, inda ikon karshe kan zabe ke hannun masu kada kuri’a.
Ta kawo misalin zaben Malam Ibrahim Shekarau a 2003, wanda ta ce ya hau mulki ba tare da wani babban jagora ba, sai dai saboda amincewar jama’a da halayensa.
Yadda Abba ya yi nasara a jihar Kano
Sanarwar ta jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf bai hau mulki saboda tallafin wasu 'yan siyasa ba. Al’ummar Kano ne suka zabe shi, ya kare nasararsa ta hanyoyin doka, sannan ya fara tafiyar da mulki da sahihiyar manufa.
Ta ce tun bayan hawansa, Abba ya sauyawa daga kasancewa mabiyi zuwa cikakken jagoran da ke gina manufofi a ilimi, gyaran hukumomi da dawo da amincewar jama’a.
Don haka, kwamishinan yada labaran ya kara da cewa bayyana Abba Kabir a matsayin wanda ke “tsaye a kan kafafun aro” kuskure ne.
Gwamnatin Kano ta jawo aya da hadisi
Gwamnatin ta bayyana cewa rikice-rikicen shugabanci, rarrabuwar kawuna da shari’o’in da ke gaban kotu sun jefa NNPP cikin mawuyacin hali.
Sanarwar ta kammala da ambaton aya daga Suratul Taubah, aya ta 51, da ke nuna cewa babu abin da zai samu mutun sai abin da Allah ya kaddara.
Ta kuma karanto wani Hadisi na Manzon Allah (SAW) kan tawakkali, inda ta ce komai yana cikin kaddarar Allah, kuma wannan ita ce hakikanin lissafin siyasar Kano.

Source: Facebook
Buba Galadima ya gargadi Abba Kabir
A wani labarin, kun ji cewa daya daga cikin dattawan NNPP, Buba Galadima ya yi gargadi ga gwamma Abba Kabir Yusuf kan sauya sheka.
Buba Galadima ya ce tun farar safiya suke da labarin masu zuga Abba Kabir ya bijirewa jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso.
Ya yi gargadi da cewa idan gwamna Abba Kabir ya ci amanar Rabiu Kwankwaso, da sannu zai gani a kwaryar tuwonsa a siyasar jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

