Ana Batun Sauya Shekar Gwamna, Jagora a APC Ya Dawo NNPP Kwankwasiyya
- Daya daga cikin jagororin APC, Hon. Aminu Aliyu Tiga ya fice daga jam'iyyarsa awanni kadan kafin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shige ta
- Hon. Tiga ta sanar da cewa ya karbi darikar Kwankwasiyya a NNPP, saboda akidar nagartar shugabanci da saka muradin jama’a a gaba
- Ya jaddada cewa akidun NNPP na zaman lafiya, daidaito da ci gaba sun yi daidai da hangen nesansa da muradunsa na siyasa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jagora a APC, Hon. Aminu Aliyu Tiga ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyarsa da ke mulkin Najeriya.
Hon Aminu Aliyu Tiga ya sanar da cewa ya koma NNPP, inda ya karbi darikar Kwankwasiyya karkashin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Source: Twitter
Hadimin Sanata Kwankwaso, Saifullahi Hassan ne ya tabbatar da haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na X.
Hon. Aliyu Tiga ya bar APC a Kano
A wata wasika da ya aike wa Shugaban mazabar Gwarmai, Karamar Hukumar Bebeji, Hon. Tiga ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bayan tunani zurfi.
Ya kara da cewa an zauna tare da yin shawarwari da magoya baya, yana mai cewa ya yi imani cewa akidun NNPP sun fi dacewa da burinsa na kyakkyawar makomar Najeriya.
A cewarsa:
“Ina da tabbacin cewa muhimman ƙimomin NNPP — zaman lafiya, daidaito da ci gaba — sun yi daidai da hangen nesana na gina ƙasa mai adalci da walwala.”
Abin da ya ja Hon. Tiga zuwa Kwankwasiyya
Hon. Tiga ya bayyana cewa abin da ya ja hankalinsa zuwa NNPP shi ne fifikon da jam’iyyar ke bai wa talakawa da haɗin kai, maimakon fifita ’yan siyasa.

Source: Twitter
Ya ce jam’iyyar na bin tafarkin siyasar jama’a wadda ke mayar da hankali kan bukatun al’umma.
A kalamansa:
“Ina matuƙar sha’awar yadda jam’iyyar ke fifita muradun talakawa a kan na masu ruwa da tsaki na siyasa."
“Haka kuma, jajircewar NNPP wajen gaskiya da bayyana gaskiya a mulki, tare da girmama juna da haƙuri, abu ne da na kae tsaye a kai.”
Ya ƙara da cewa matakin nasa ya nuna tsayuwarsa kan akida maimakon siyasar son rai, yana mai bayyana fatan ba da gudunmawa wajen bunƙasa jam’iyyar.
Hon Tiga ya ce:
“Ina farin cikin shiga jam’iyyar da ke sanya kida a gaba, tare da mayar da mulki ga jama’a, ina fatan ba da gudunmawa wajen gina NNPP tare da haɗin gwiwar ’yan jam’iyya domin cimma manufofinmu na bai ɗaya.”
Abba ya yi riko da Kwankwasiyya
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar NNPP ba ya nufin rabuwa da Kwankwasiyya.
Wannan karin haske ya zo ne awanni kaɗan bayan sanarwar da ta fitar, tana tabbatar da cewa Gwamnan ya bar jam’iyyar NNPP sakamakon matsalolin cikin gida.
Sanarwar da Hadimin Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta kara da bayanin cewa ficewa daga NNPP ba ya nufin za a sauka daga tsarin Kwankwasiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

