Arewa: Matasan APC Sun Cire Tsoro, Sun Fadawa Tinubu Illar Sauya Shettima a 2027

Arewa: Matasan APC Sun Cire Tsoro, Sun Fadawa Tinubu Illar Sauya Shettima a 2027

  • Kungiyar APC Youth Parliament North East ta yi karin haske game da jita-jitar da ake yadawa kan maganar sauya Kashim Shettima
  • Shugaban kungiyar, Kabiru Garba Kobi daga Bauchi, ya zargi wasu 'yan siyasa da yada rade-radin saboda cimma burinsu
  • Kabiru Kobi ya bayyana haka yayin zantawa da wakilin Legit Hausa a ranar Lahadi 25 ga watan Janairun 2026 da muke ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Kungiyar 'APC Youth Parliament North East' ta yi martani mai zafi ga wasu yan siyasa game da kujerar Kashim Shettima da tazarcen Bola Tinubu.

Kungiyar ta bayyana damuwa game da maganar da ake ta yadawa da ba ta da tushe kan sauya Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima.

Matasan APC sun dura kan masu neman a cire Shettima
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (hagu), Kabiru Kobi, shugaban kungiyar matasan APC (tsakiya), da Kashim Shettima (dama). Hoto: @officialABAT, @KashimSM.
Source: Twitter

Shugaban kungiyar, Kabiru Garba Kobi daga jihar Bauchi shi ya bayyana haka yayin zantawa da wakilin Legit Hausa a ranar Lahadi 25 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: APC ta yi magana kan sauya Shettima a zaben 2027

Hakan bai rasa nasaba da yawan maganganu game da Kashim da kuma yada cewa za a sauya shi da Kirista daga Arewacin Najeriya, cewar Punch.

Martanin matasan APC ga Dogara, tsofaffin yan majalisa

Kabiru Kobi ya bayyana damuwa game da matsayar yan siyasar inda ya ce wasunsu sun butulce wa alherin da aka yi musu.

Ya ce daman suna gaba da gwamnatin Bola Tinubu tun farko sai yanzu Allah ya tona musu asiri suka bayyana mummunan manufarsu.

Ya ce:

"Akwai wandanda aka biya kudi suna kiran a cire Sanata Kashim Shettima a maye gurbinsa da shi, kai da kake so a baka mataimakin shugaban kasa, kuma ba a kai wata biyu ba, sai ka sake turo wasu suna ikirarin cewa ba su goyon bayan gwamnati.
"To wace maganarsa ce abin dauka, muna son fada wa mutane cewa wadannan ba suna fada da Kashim Shettima ba ne, suna fada ne da gwamnatin Bola Tinubu.
Matasan APC sun goyi bayan Tinubu, Shettima
Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Kashim Shettima.
Source: Twitter

Garba Kobi ya yi Allah wadai da wasu maganganu da ake yadawa inda ya ce gwamnatin Bola Tinubu ba ta dogara da su ba daman.

Kara karanta wannan

Dogara: Kiristan da aka ce zai maye Shettima a 2027 ya fito ya yi magana

"Muna Allah wadai da wadannan kalaman nasu, kuma gwamnatin Bola Tinubu da APC ba ta dogara da su ba, haka kuma ba su ta ce zabe.
"Shettima mutum ne da ya fito daga Borno, ya hada kan Arewa maso Gabas, shi kuma tun farko Dogara ya ki jinin Muslim/Muslim amma tausayi suka ji suka ba shi mukami a gwamnatin."

- Kabiru Kobi

Kabiru Kobi ya shawarci masoyan Kashim da su godewa Allah saboda gaskiya ta yi halinta ganin akwai makiyansa kuma yanzu Allah ya bayyana su.

Ya ce su masoya Kashim da APC da Arewa maso Gabas suna murna da Allah ya tona musu asiri, kuma Allah ya ci gaba da tona asirin makiya talakawan Najeriya da APC.

APC ta magantu kan jita-jitar sauya Shettima

Mun ba ku labarin cewa ana ci gaba da yada jita-jitar cewa wai Bola Tinubu yana shirin sauya mataimakinsa, Kashim Shettima kafin 2027.

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi magana kan batun da ke yawo na shirin sauya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a zaben 2027.

Mai magana da yawun bakin APC na kasa, Felix Morka, ya karyata rahoton da kuma bayyana abin da jam'iyyar ta sanya a gaba a wannan lokacin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.