Wata 6 bayan Shiga ADC, Tsohon Sanata Ya Dawo PDP, Ya Jingina Zargi ga Tambuwal
- Tsohon Sanatan Sokoto ta Gabas ya sanar da ficewarsa daga ADC tare da komawa jam’iyyar PDP gabanin zaɓen 2027
- Sanatan ya zargi Aminu Waziri Tambuwal da rashin jajircewa da jagoranci a ADC, yana cewa hakan ya bar jam’iyyar cikin ruɗani
- Sai dai PDP a Sokoto ta ce ba ta da masaniya kan shigowar sa jam’iyyar, tana musanta cewa sun karɓe shi a hukumance
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Tsohon ɗan majalisar tarayya kuma Sanatan Sokoto ta Gabas, Abubakar Umar Gada, ya sanar da komawarsa jam’iyyar PDP.
Sanata Gada ya tabbatar da haka ne a ranar Asabar, gabanin zaɓen shekarar 2027, bayan makonni ana rade-radin makomarsa a siyasa.

Source: Facebook
Tsohon sanata ya bar ADC zuwa PDP
Gada ya bayyana hakan ne a wani taron magoya bayansa a Sokoto, inda ya ce matakin da ya ɗauka na komawa PDP ya samo asali ne daga burinsa na sake farfaɗo da jam’iyyar a jihar, cewar Punch.
Ya zargi Sanata Aminu Waziri Tambuwal, da gaza nuna jajircewa da jagoranci a jam’iyyar ADC, duk da cewa sun yi niyyar tafiya tare a cikinta tsawon watanni shida.
Gada, wanda ya wakilci Sokoto ta Gabas a majalisar dattawa daga 2007 zuwa 2011 a ƙarƙashin PDP, kuma ya koma ADC a 2025, ya ce an ɗauke shi da Tambuwal a matsayin jagororin jam’iyyar a Sokoto.
Ya ce:
"Ni da Sanata Tambuwal an ɗauke mu a matsayin jagororin tafiyar, amma shugabanci yana buƙatar kusanci da jama’a da jajircewa."
Gada ya ce Tambuwal bai taɓa zuwa ya zauna da su domin gina jam’iyyar ba, lamarin da ya jefa ADC cikin ruɗani a Sokoto.
Ya kuma zarge shi da rikice-rikicen siyasa, yana cewa yana tattaunawa da APC a ɓangare guda, sannan kuma ana raɗe-raɗin cewa ana kallonsa a matsayin mataimakin ɗan takarar Peter Obi.

Source: Original
Dalilin komawar Sanata Gada PDP
A cewarsa, wannan rashin tabbas ya sa ya yanke shawarar “ɗaukar makomarsu da hannunsu” ta hanyar komawa PDP, cewar Channels TV.
Ya kuma soki abin da ya kira rashin godiya a siyasa, yana tunatar da irin damar da Tambuwal ya samu tun daga zama Kakakin Majalisar Wakilai har zuwa gwamna sau biyu.
A gefe guda, magoya bayan PDP da suka hada da Alhaji Hamza Yabo sun bayyana ficewar Gada a matsayin wani babban mataki na farfaɗo da jam’iyyar bayan shan kaye a zaɓen 2023.
Sai dai sakataren yaɗa labaran PDP a Sokoto, Hassan Sayinnawal, ya musanta ikirarin, yana cewa jam’iyyar ba ta da labarin shigowar Sanata Gada.
Ya ce babu wani mataki da aka ɗauka a mazabarsa, ƙaramar hukumarsa, ko ma a matakin jiha da ƙasa da ke nuna cewa Gada ya koma PDP.
Dan Atiku ya gudu daga PDP zuwa APC
Kun ki cewa daya daga cikin 'ya'yan Alhaji Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya.
Abubakar Atiku Abubakar wanda aka fi sani da Abba ya samu tarba daga wajen jiga-jigan jam'iyyar APC bayan sauya shekarsa.
Ya bayyana dalilin da ya sa ya zabi shiga jam'iyyar APC tare da goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Asali: Legit.ng

