Babu makawa APC ce zata kawo jihar Sokoto – Sanata Gada

Babu makawa APC ce zata kawo jihar Sokoto – Sanata Gada

- Sanata Abubakar Gada ya bayyana cewa yana da yakinin samun tikitin APC

- Ya jadadda cewa babu makawa jam’iyyar ce zata lashe zaben gwamna a jihar Sokoto

- Gada yace yana so ceto jihar daga turbar hallaka

Sanata Abubakar Gada ya bayyana cewa yana da yakinin samun ikitin APC sannan kuma ya lashe zaben gwamna a jihar Sokoto.

Da yake Magana a sakatariyar APC na kasa dake Abuja bayan mayar da fam dinsa, Sanata Gada yace duba ga harkokin siyasarsa, yana da abuna ke bukata wajen hana jihar Sokoto daga durkushewa ta fannin tattalin arziki.

Babu makawa APC ce zata kawo jihar Sokoto – Sanata Gada
Babu makawa APC ce zata kawo jihar Sokoto – Sanata Gada
Asali: Facebook

“A tarihi, ana matukar mutunta Sokoto zuciyar sarauta, ba wai a Najeriya kadai ba harma a fadin duniya an san cewa Sokoto na da tsohuwar tarihi na shugabanci mai inganci, zaman lafiya da mutunci.

“Ina Magana ne akan shekaru 200 da suka shige, kalli halin da muka riski kanmu ciki a yau, an hofantar da tarihin siyasarmu. An dakushe mafarkin yaranmu don haka ina ganin wannani wani kaalubale ne ya zama dole na taimaka wajen ceto mutane na,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Jirgin Ali Modu Sheriff ta sabbaba kulle filin jirgin saman Abuja

Yace APC ce zata ci gaba da mulki: asu dakushe mana cigabanmu sun fice don haka mn shirya ma sabon damara. Mu, masu fada aji a Sokoto mun aika wasika ga shugaban jam’iyyarmu na kasa da ya bamu sabon jagora saboda Gwamna Tambuwal ya fice da mutanensa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) a turance ta karin haske game da batun yiwuwar daga zabukan gama gari na shekarar 2019 da take shirin gudanarwa a shekarar 2019.

Kamar dai yadda muka samu, a cikin wata sanarwar da jami'in hulda da jama'a na hukumar, Mista Rotimi Oyekanmi ya sa wa hannu ya kuma rabawa manema labarai yace hukumar bata da wani kuduri na zahiri ko na boye na daga zaben mai zuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel