Magana Ta Kare: Kwamishina Ya Dauki Layinsa tsakanin Abba Kabir da Kwankwaso
- Kwamishinan gwamnatin Kano, Adamu Aliyu Kibiya ya kama layinsa a siyasar jihar bayan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf
- Kibiya ya ce har yanzu yana tsaye kan akidu da manufofin jam'iyyar NNPP mai adawa a kasa da Kwankwaso ya assasa
- Ficewar gwamnan ta haifar da sabon tsari a siyasar Kano, inda ‘yan jam’iyya da dama ke bayyana inda suka dosa a halin yanzu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano – Kwamishinan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci na Kano, Adamu Aliyu Kibiya, ya kama layinsa a siyasar jihar.
Adamu Aliyu Kibiya ya fito fili ya sake jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar NNPP da kuma jagoranta na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Twitter
Kwamishina ya kama layi tsakanin Abba, Kwankwaso
Alhaji Kibiya ya bayyana matsayarsa ne a cikin wata wasika da ya aikawa Kwankwaso a ranar Asabar 24 ga watan Janairun 2026, cewar Punch.
Kibiya ya yi alkawarin ci gaba da goyon baya da hadin kai da NNPP, yana mai bayyana jam’iyyar a matsayin wacce aka gina bisa jagoranci mai la’akari da talakawa, adalci a zamantakewa da ka’idojin dimokuradiyya.
Kwamishinan ya ce sababbin sauye-sauyen siyasa, musamman ficewar gwamnan daga NNPP, sun jefa ‘yan jam’iyyar cikin damuwa, lamarin da ya sa ya ga dacewar fito wa ya fayyace matsayarsa.
Ya ce:
“Duk da matsayin da nake kai a cikin gwamnati a yanzu, ina ci gaba da tsayawa daram kan manufofi, ka’idoji da hangen nesa da aka kafa jam’iyyar NNPP a kai.”

Source: Twitter
Dalilin kwamishina na bin Kwankwaso da NNPP
Kibiya ya kara da cewa akidu da darajojin jam’iyyar NNPP a karkashin jagorancin Kwankwaso su ne ginshikin tunaninsa na siyasa da kuma hidimarsa ga al’umma.
Har ila yau, ya yaba da jajircewar Kwankwaso a siyasa da irin sadaukarwar da ya yi tsawon lokaci, yana mai cewa shugabancinsa na ci gaba da zama abin koyi da kwarin gwiwa ga miliyoyin ‘yan Najeriya.
A cewarsa:
“Ina so na tabbatar maka kai tsaye da cikakkiyar biyayya ta ga jam’iyyar NNPP, tare da girmamawa da goyon baya ga jagorancinka da shawarwarinka.”
Wannan matsaya ta Kibiya na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar rudani a cikin NNPP a jihar Kano bayan Gwamna Abba Kabir ya fice daga jam’iyyar, bayan makonni na rade-radin siyasa kan makomarsa.
Rahotanni sun nuna cewa ficewar gwamnan ta haifar da sabon sauyi a siyasar jihar, inda ‘yan siyasa da masu rike da mukaman jam’iyya ke bayyana matsayinsu, wasu na bin sabon layin gwamnan, yayin da wasu ke nanata biyayya ga Rabiu Kwankwaso.
Kwamishina ya fadi wadanda ke tare da Abba
Mun ba ku labarin cewa Kwamishina a gwamantin Abba Kabir ya yi magana a kan yadda Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ke yi wa gwamnan.
Aliyu Isa Aliyu ya ce Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso bai taba bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gaza a wajen sauke nauyin al'umma ba.
Ya bayyana haka ne a lokacin da 'yan NNPP ke bin bayan Gwamna da ya sauya sheka, yayin da wasu ke tare da tsohon gwamna Kwankwaso.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

