Zance Ya Kare: 'Yan Majalisar Kano 22 Sun Bayyana Matsayarsu kan Tafiyar Gwamna Abba

Zance Ya Kare: 'Yan Majalisar Kano 22 Sun Bayyana Matsayarsu kan Tafiyar Gwamna Abba

  • Mambobin majalisar dokokin Kano 22 sun yanke shawarar bin tafiyar Gwamna Abba Kabir Yusuf a dambarwar da ke faruwa a jihar
  • Kakakin Majalisar dokokin Kano, Rt. Hon. Isma'il Falgore, ya jagoranci wadannan mambobi sun fice daga jam'iyyar NNPP
  • Sun kuma tabbatar da cewa za su jira umarni na gaba kan matakin da ya kamata su dauka daga Mai girma gwamnan Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - 'Yan majalisar dokokin jihar Kano 22 sun dauki matsaya kan dambarwar siyasar da ke faruwa, lamarin da ya jawo ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP.

Mambobin majalisar guda 22 sun tabbatar da ficewarsu daga jam'iyyar NNPP domin nuna goyon baya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Majalisar dokokin Kano.
Yan Majalisar dokokin jihar Kano na tsakiyar zama a zauren Majalisa Hoto: Kano House of Assembly
Source: Facebook

'Yan Majalisa 22 na tare da Gwamna Abba

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kakakin Majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Matasan Kwankwasiyya sun shirya bin gwamna Abba, sun saka sharadi

Ya bayyana cewa mambobin majalisar sun dauki wannan matakin ne domin sake jaddada biyayyarsu ga gwamnatin Abba Gida-Gida.

A cewar sanarwar, wannan sauya sheka na da nufin karfafa tafiyar siyasar gwamnan biyo bayan ficewarsa daga NNPP.

Jerin 'yan majalisar Kano da suka bi Abba

Yan Majalisar da suka bar NNPP sun hada da:

1. Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore (Shugaban Majalisa - Rogo)

2. Rt. Hon. Muhammad Bello Butu Butu (Mataimakin Shugaban Majalisa - Tofa/Rimin Gado)

3. Hon. Lawan Hussain (Shugaban Masu Rinjaye - Dala)

4. Hon. Garba Shehu Fammar (Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye - Kibiya)

5. Hon. Muddasir Ibrahim Zawachiki (Babban Mai Tsawatarwa - Kumbotso)

6. Hon. Zakariyya Abdullahi Nuhu (Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye - Gabasawa)

7. Hon. Lawal Tini (Ajingi)

8. Hon. Musa Tahir Haruna (Albasu)

9. Hon. Ali Lawan Alhassan (Bagwai/Shanono)

10. Hon. Ali Muhammad Tiga (Bebeji)

11. Hon. Hafiz Gambo (Bunkure)

12. Hon. Rabiu Shuaibu (Dawakin Kudu)

13. Hon. Tukur Mohammed (Fagge)

14. Hon. Murtala Muhammad Kadage (Garko).

Kara karanta wannan

Sakon da APC ta fara Aika wa Gwamna Abba bayan ya fice daga NNPP

15. Hon. Abdulmajid Isah Umar (Gwale)

16. Hon. Engr. Ahmad Ibrahim (Karaye)

17. Hon. Alhassan Zakari (Kura/Garun Malam)

18. Hon. Suleiman Mukhtar Ishaq (Madobi)

19. Hon. Abdulhamid Abdul (Minjibir)

20. Hon. Muhammad Ibrahim (Rano)

21. Hon. Kabiru Sule Dahiru (Tarauni)

22. Hon. Ali Abdullahi Manager (Wudil).

Rt. Hon. Isma'il Falgore.
Kakakin majalisar dokokin Kano, Rt. Hon. Isma'il Falgore tare da Gwamna Abba Kabir Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wace jam'iyya 'yan majalisar za su koma?

Sanarwar ta kara da cewa ‘yan majalisar sun amince da matakin gwamnan na barin NNPP, kuma suna jiran karin umarni kan mataki na gaba da za su dauka a siyasance.

Duk da cewa Gwamna Yusuf bai bayyana takamaiman jam’iyyar da zai koma ba, akwai alamun cewa yana kan hanyar komawa jam’iyyar APC.

Idan hakan ta tabbata, ana sa ran majalisar mai mambobi 40 za ta koma karkashin ikon jam’iyyar APC, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Gwamnatin Kano ta gargadi magoya baya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ce ba za ta lamunci taba mutuncin jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso ba.

Kara karanta wannan

Kwamishinoni 2 sun yanke shawara, sun zabi wanda za su bi tsakanin Abba da Kwankwaso

Mai magana da yawun gwamnan Kano , Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya fitar da wannan gargadi a ranar Litinin, a taron raba babura da ya guda a gidan gwamnati.

Ya bayyana Kwankwaso a matsayin jagoran siyasa wanda dole ne a mutunta matsayinsa a siyasar Kano, ba tare da la’akari da sauyin siyasar da ake ciki ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262