Badaru Ya Gana da Kwankwaso bayan Ficewar Abba daga NNPP? An Gano Gaskiya

Badaru Ya Gana da Kwankwaso bayan Ficewar Abba daga NNPP? An Gano Gaskiya

  • Tsohon Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi karin haske kan jita-jitar cewa ya gana da Rabiu Musa Kwankwaso
  • Badaru ya ce hoton da ake yadawa tsoho ne da aka dauka shekaru 3 da suka wuce, lokacin da suka haɗu a wani filin jirgin sama
  • Haka zalika tsohon gwamnan ya sake nanata cikakken goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu da shugabancin jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Tsohon Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi magana kan rahoton ganinsa da Rabiu Kwankwaso.

Badaru ya fito ya karyata rahotannin da ke yawo cewa ya yi wata ganawa da jagoran jam’iyyar NNPP kuma 'dan takarar shugaban kasa a 2023.

Badaru ya karyata alaka da Kwankwaso
Tsohon Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar. Hoto: Defence Headquaters Nigeria.
Source: Twitter

Gaskiyar magana kan ganawar Badaru da Kwankwaso

Wannan bayani ya fito ne a cikin wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai da Yada Bayanai, Kwamared Mati Ali, ya bayyana a Facebook.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Kwamishina ya dauki layinsa tsakanin Abba Kabir da Kwankwaso

Badaru ya bayyana rahotannin da ke yaduwa a kafafen sada zumunta a matsayin marasa tushe kuma masu ruɗani, inda ya jaddada cewa har yanzu cikakken mamba ne na jam’iyyar APC, kuma yana da cikakken biyayya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cewar sanarwar, hoton da ake yadawa a yanar gizo wanda ake ikirarin yana nuna wata sabuwar ganawa tsakanin Badaru da Kwankwaso, tsohon hoto ne da aka ɗauka tun ranar 18 ga Fabrairu, 2023.

Kwamared Mati Ali ya bayyana cewa hoton an ɗauke shi ne a lokacin da yan siyasar biyu suka haɗu kwatsam a filin jirgi, ba tare da wata ganawa ta siyasa ko shiri a tsakaninsu ba.

Sanarwar ta ce:

“Mun ga ya dace mu ja hankalin al’umma kan wani hoto da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ƙoƙarin nuna cewa tsohon Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya gana da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
“Don kauce wa ruɗani, wannan hoton tsoho ne. An ɗauke shi ne ranar 18 ga Fabrairu, 2023, lokacin da suka haɗu a filin jirgi."
Badaru ya fayyace ganawarsa da ake yadawa da Kwankwaso
Mohammed Badaru ya hadu da Sanata Rabiu Kwankwaso a filin jirgi a Abuja a 2023. Hoto: Hon. Saifullahi Hassan.
Source: Facebook

A ina Badaru yake tsawon wata guda?

Sanarwar ta ƙara da cewa Badaru ya shafe fiye da wata guda yana ƙasashen waje, kuma har yanzu bai dawo Najeriya ba, lamarin da ke tabbatar da cewa ba zai yiwu a ce an yi wata ganawa ba.

Kara karanta wannan

Tijjani Gandu ya yi wa Kwankwaso sabuwar waka Abba na fita daga NNPP

Tsohon Ministan ya bukaci jama’a da su yi watsi da rahoton ƙarya, tare da gargadin masu amfani da kafafen sada zumunta da su daina sake yada tsofaffin abubuwa da ake amfani da su wajen kirkirar labaran bogi.

A karshe, Badaru ya sake jaddada cikakken biyayyarsa ga jam’iyyar APC, tare da nuna goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, manufofinsa da shugabancin jam’iyyar baki daya.

Badaru ya musanta shirin barin APC

Kun ji cewa tsohon ministan tsaro a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya yi karin haske game da rade-radin cewa zai bar APC.

Badaru ya karyata jita-jitar cewa yana shirin barin APC zuwa jam’iyyar ADC bayan ya yi murabus daga kujerar minista.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da mambobin APC su yi watsi da rahotannin, yana cewa ba shi da niyyar ficewa daga jam’iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.