Matasan Kwankwasiyya Sun Shirya Bin Gwamna Abba, Sun Saka Sharadi

Matasan Kwankwasiyya Sun Shirya Bin Gwamna Abba, Sun Saka Sharadi

  • Wasu kungiyoyin matasan Kwankwasiyya a Kano sun ce za su iya tafiya da Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan ficewarsa daga NNPP
  • Sun danganta matsayinsu da abin da suka kira wariya da rashin saka wa matasan da suka dade suna hidima a Kwankwasiyya
  • Kungiyoyin sun ce idan gwamnati ta gyara wadannan matsaloli, za su ba ta cikakken goyon baya a raka Gwamna zuwa sabuwar jam'iyyarsa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wasu kungiyoyin matasan Kwankwasiyya a Jihar Kano sun bayyana aniyarsu ta bin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya fice daga NNPP, amma sun ce hakan zai dogara ne da cika wasu sharudda.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da murabus daga jam'iyyar NNPP ne ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar a mazabar Diso-Chiranchi da ke karamar hukumar Gwale.

Kara karanta wannan

'Abin da na fada wa Abba Kabir game da butulce wa Kwankwaso - Sanatan NNPP'

Wasu matasan Kwankwasiyya za su bi Gwamnan Kano
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf tare da Madugun Kwankwasiyya Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A sanarwar da jaridar Punch ta ruwaito, Gwamna Abba ya ce murabus din zai fara aiki daga ranar 25 ga Janairu, 2026 saboda dalilan matsaloli a jam'iyya.

Dalilan Gwamna na ficewa daga NNPP

Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamnan Kano ya danganta matakin barin NNLL da tsanantar rikicin cikin gida da sabanin shugabanci da kuma shari’o’in da ke gaban kotuna.

A cewarsa:

“A baya-bayan nan, jam’iyyar ta fuskanci kalubale na cikin gida sakamakon rikice-rikicen shugabanci da kuma shari’o’in da ke jiran hukunci a gaban kotuna."

Gwamnan ya kara da cewa lamarin ya jawo rarrabuwar kai da raunana hadin kan jam’iyyar da ke cikin kalubalen shugabanci iri-iri.

Matasan Kwankwasiyya za su ba Abba

Da yake jawabi a wani taron tattaunawa da matasa a Kano, wakilan kungiyoyin Kwankwasiyya sun ce ba su da matsala da Gwamna Abba a matsayin mutum.

Aminu Abdullahi, wanda aka fi sani da Alhaji Warkal, ya ce matasan za su iya tafiya da gwamnan muddin gwamnatinsa ta rika daukar matasa a matsayin abokan hulda.

Kara karanta wannan

Kwamishinoni 2 sun yanke shawara, sun zabi wanda za su bi tsakanin Abba da Kwankwaso

Ya kara da bayyana cewa amma suna da damuwa a kan abin da suka kira ware su daga harkokin yanke shawara da shirye-shiryen gwamnatin da suka yi wa wahala.

Matasan Kwankwasiyya sun gindaya wa Gwamna sharadi
Gwamna Abba Kabir Yusuf a wani taron ranar ma'aikata a Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ya ce:

“Ba mu ce ba za mu taba tafiya da shi ba. Za mu yi tafiya da Gwamna Abba Kabir Yusuf idan gwamnati ta dauki matasa da gaske, ta faranta masu a cikin mulki."

Aminu Abdullahi ya kara da cewa matasa da dama da suka taka rawar gani wajen nasarar Kwankwasiyya da NNPP a zaben 2023 suna jin an yi watsi da su bayan an samu nasara. A kalamansa:

“Wadannan matasa sun sadaukar da lokacinsu, karfinsu da dukiyarsu wajen kawo gwamnati kan mulki. Amma bayan nasarar, ba a saka su cikin shirye-shirye, shawarwari ko damar da ta shafe su ba,” ya ce.

A cewarsa, rashin shigar da matasa cikin mulki na kara haddasa takaici a tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya a Kano, yana mai jaddada cewa shigar da matasa cikin harkokin gwamnati na taimakawa wajen rage aikata laifuffuka da tashin hankali a al’umma.

Ya kuma karyata zargin cewa wasu ‘yan siyasa na tilasta wa matasan daukar wani bangare, yana mai cewa matsayinsu ya ta’allaka ne kan muradi da abin da suke tsammani daga gwamnati.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya fallasa yadda aka zuga Abba kan rabuwa da Kwankwaso

Aminu ya ce:

“Wannan ba batun tilasta wa kowa ba ne. Siyasa batun anfani ce. Idan gwamnati ta saurari matasa ta tallafa musu, su ma za su tallafa wa gwamnati."

Ya ce tattaunawar da aka yi da kungiyoyin matasa daban-daban ta nuna cewa akwai yunkurin marawa gwamnan baya, muddin an magance korafe-korafen da suka gabatar.

Hadimin Gwamnan Kano ya yi murabus

A baya, mun wallafa cewa Mai bai wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, shawara ta musamman a kan harkokin siyasa, Sunusi Surajo Kwankwaso, ya yi murabus daga mukaminsa.

Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam’iyyar NNPP, yayin da ake sa ran zai sanar da sabuwar jam’iyyar da zai koma.

Ya bayyana haka ne ta faifan bidiyo da aka saki ranar Juma’a, 23 ga watan Janairu, 2026, wanda mai taimaka wa Sunusi Kwankwaso a harkokin yada labarai, Saifullahi Hassan ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng