Kwamishinan Abba Ya Jero Mutanen da ba Su tare da Gwamna a Jihar Kano

Kwamishinan Abba Ya Jero Mutanen da ba Su tare da Gwamna a Jihar Kano

  • Kwamishina a gwamantin Kano, Aliyu Isa Aliyu ya yi magana a kan yadda Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ke yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Farfesa Aliyu ya ce Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso bai taba bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gaza a wajen sauke nauyin al'umma ba
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da 'yan NNPP ke bin bayan Gwamna da ya sauya sheka, yayin da wasu ke tare da tsohon gwamna Kwankwaso

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kwamishinan Bunkasa Harkar Dabbobi na Jihar Kano, Alhaji Aliyu Isa Aliyu, ya fayyace kallon da jagoran Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso ke yi wa Gwamnan Abba Kabir Yusuf.

Tsohon malamin jami'an ya ce har yanzu, Sanata Kwankwaso bai taba suka ko bayyana gazawar Gwamnan Kano wajen sauke nauyin al'umma da ke wuyansa ba.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya fallasa yadda aka zuga Abba kan rabuwa da Kwankwaso

Kwamishina a Kano ya ce babu baraka a tsakanin Abba da Kwankwaso
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf tare da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso riƙe da kyautar girmamawa
Source: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Aliyu Isa Aliyu ya wallafa a shafinsa na Facebook yayin da siyasar Kano ta dauki zafi.

Bayanin matsayar jagora Kwankwaso

A cewar Kwamishinan, har zuwa yau babu wani jawabi, taro ko rubutaccen bayani da Jagora Rabiu Musa Kwankwaso ya taba yi don kushe Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Wannan bayani na zuwa ne domin karyata jita-jitar da ke yawo cewa akwai sabani kai tsaye tsakanin Jagoran da Gwamnan.

Aliyu Isa Aliyu ya jaddada cewa Sanata Kwankwaso mutum ne mai ka’ida da tsari, wanda ke fadin albarkacin bakinsa a idan akwai matsala.

Rashin bayyana matsalar, a cewarsa, hujja ce da ke nuna gamsuwa da shugabancin da ake yi a halin yanzu.

Ya kara da cewa jam’iyya na da hanyoyin warware matsala a cikinta, ba tare da bata suna ko tayar da rudani a idon jama’a ba.

Kara karanta wannan

Abba ya rike akidar Kwankwasiyya gam duk da rabuwar da jam'iyyar NNPP

Su wane ne marasa goyon bayan Abba?

Kwamishinan ya bayyana cewa akwai wasu rukunin ‘yan NNPP masu rajista da ke cikin siyasa amma ba sa jituwa da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya ce rukuni na farko su ne wadanda ke fatan samun damar shiga baitul malin jiha ba tare da iyaka ba, tare da matsin lamba cewa Gwamna ya yi wa’adi guda daya kacal.

Rukuni na biyu kuwa su ne wadanda aka ba mukamai amma suka kasa nuna kwarewa a aikinsu, daga bisani suka dauka cewa ba a musu adalci ba.

Aliyu Isa Aliyu ya ce Kwankwaso ya gamsu da aikin Abba
Gwamna a Kano, Abba Kabir Yusuf yana jawabi Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ya kara da cewa sai kuma mutanen da suke ganin ba su amfana da gwamnatin kai tsaye ba, wanda hakan ya sa suke nuna rashin gamsuwa da gwamnatin Abba na daga cikin waɗanda ba sa goyon bayansa.

Haka kuma a cewar Aliyu, ‘yan takara na Majalisar Jiha, Wakilai ko Dattawa na ganin kusantar Gwamna na iya kawo cikas ga burinsu, musamman inda tsofaffin ‘yan majalisa daga yankunansu suka fice daga NNPP.

Kara karanta wannan

"Ba za a ci amana da ni ba:" Kwankwaso ya ajiye mukaminsa a gwamnatin Abba

Rukuni na karshe su ne masu tambayar dalilin da ya sa wasu ke rike da mukamai, alhali su ba su samu ba, lamarin da ke kara tayar da rashin fahimta a jam’iyyar.

Gwamnatin Kano na tare da Kwankwasiyya in ji D-Tofa

A wani labarin, mun wallafa cewa Gwamnatin Jihar Kano ta fayyace cewa ficewar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi daga jam’iyyar NNPP ba ta nufin ya bar tsarin Kwankwasiyya.

Wannan karin haske ya zo ne awanni kaɗan bayan gwamnatin jihar ta sanar da ficewar gwamnan daga NNPP, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar jihar da kasa baki ɗaya.

A wani sako da hadimin gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa, ya fitar bayan ficewar Abba daga NNPP, ya bayyana cewa barin jam’iyya ba yana nufin rabuwa da akida ko tafarkin siyasa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng