2027: Ana So Kwankwaso Ya Hada kai da Barau Su Kifar da Abba a Kano

2027: Ana So Kwankwaso Ya Hada kai da Barau Su Kifar da Abba a Kano

  • 'Dan jam’iyyar APC, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, ya ce fitar Abba Kabir Yusuf daga NNPP ya zama babban cin amana ga Rabiu Musa Kwankwaso
  • Ya bayyana cewa sun riga sun dauki Sanata Barau Jibrin a matsayin dan takara a Kano, yana mai cewa hadin kan Barau da Kwankwaso zai iya kifar da Abba
  • Dan Bilki ya ce tasirin Sanata Rabiu Kwankwaso a Kano bai gushe ba, yana mai jaddada cewa masu bin Abba suna bin bukatar kansu ne ba akida ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano - Dan jam’iyyar APC, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, ya yi kakkausar magana kan fitar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyar NNPP da kuma shirin komawarsa APC mai mulki.

'Dan Bilki ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi, a daidai lokacin da siyasar Kano ke kara daukar zafi biyo bayan sanarwar fitar Abba daga NNPP tare da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya fallasa yadda aka zuga Abba kan rabuwa da Kwankwaso

Rabiu Musa Kwankwaso, Barau Jibrin da Abba Kabir Yusuf
Sanata Rabiu Kwankwaso, Barau Jibrin da gwamna Abba Kabir Yusuf. Hoto: Barau I. Jibrin|Saifullahi Hassan|Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Dan Bilki Kwamanda ya yi ne a wani bidiyo da shafin Kwankwasiyya Reporters TV ya wallafa a Facebook.

Zargin cin amanar Rabiu Kwankwaso

A cewar Dan Bilki Kwamanda, Abba Kabir Yusuf ya aikata cin amana mai girma ga jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Ya ce wannan ba karamin cin amana ba ne, la’akari da yadda Kwankwaso ya taka rawa wajen gina tafiyar siyasar Abba tun daga tushe.

'Dan Bilki ya ce Kwankwaso ya ajiye manyan mutane a baya, ya dauki Abba Kabir duk da cewa ba a san shi sosai a Kano ba, ya ba shi damar tsayawa takarar gwamna.

Barau, Kwankwaso da zaben 2027

Dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa sun riga sun dauki Sanata Barau Jibrin a matsayin dan takarar da za su zaba a Kano a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Abba ya rike akidar Kwankwasiyya gam duk da rabuwar da jam'iyyar NNPP

A fatan da ya yi, ya ce da ace Kwankwaso zai fito ya ce Barau ne dan takarar gwamna, kafin karfe 10:00 na safe, da an riga an kayar da Abba Kabir.

Ya ce duk da cewa Barau ba dan NNPP ba ne a yanzu, hakan ba zai hana hadin kan ‘yan Barau da ‘yan Kwankwaso ba wajen kalubalantar Abba a zaben 2027.

Sanata Barau Jibrin a Abuja
Sanata Barau Jibrin a Majalisar dattawa. Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Ya jaddada cewa Barau bai taba sukar Kwankwaso ba, yana mai bayyana shi a matsayin mutum mai hakuri, halin kirki da ya fito daga gidan manya.

Dan Bilki ya amince da karfi da tasirin Rabiu Musa Kwankwaso a siyasar Kano, yana mai cewa duk wanda ya ce Kwankwaso ba shi da jama’a, to karya yake yi.

An ce an ta zuga Abba ya bar Kwankwaso

A wani labarin, kun ji cewa daya daga cikin jagororin jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya yi magana kan yadda Abba Kabir Yusuf ke shirin shiga APC.

Ya bayyana cewa tun farkon rantsar da Abba Kabir Yusuf wasu mutane ke zuga shi ya rabu da Rabiu Kwankwaso duk da sun dade tare.

Buba Galadima ya karyata rade-radin da ke cewa matsaloli sun yi yawa a jam'iyyar NNPP, inda ya ce hukumar INEC ta san da zamansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng