"Za Su Sha Mamaki"; Gwamna Makinde ya Hango Makomar PDP a Zaben 2027
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi tsokaci kan masu ganin jam'iyyar PDP ta mutu murus a fagen siyasar Najeriya
- Seyi Makinde ya bayyana cewa jam'iyyar PDP na nan daram da karfinta kuma ba ta mutu ba kamar yadda wasu kde tunani
- Gwamna Seyi Makinde ya bayyana cewa jam'iyyyar PDP ta shirya ba mara da kunya a babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ogun - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi magana kan shirin jam'iyyar PDP gabanin babban zaben 2027.
Gwamna Seyi Makinde ya bayyana cewa jam’iyyar na nan daram kuma a shirye take ta ba masu sukar ta mamaki gabanin zaben gama gari na 2027.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Makinde ya yi wannan jawabi ne a taron masu ruwa da tsaki na PDP a yankin Kudu maso Yamma da aka gudanar a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun a ranar Juma'a 23 ga watan Janairun 2026.
Jiga-jigan PDP sun hadu a Ogun
Taron masu ruwa da tsaki na PDP a Kudu maso Yamma ya samu halartar shugabannin jam’iyyar da masu rike da mukaman siyasa daga jihohin Legas, Ogun, Oyo, Ondo, Osun da Ekiti.
Haka kuma, shugabannin jam’iyyar sun karɓi wasu kungiyoyi biyu da suka sauya sheƙa daga jam’iyyun APC da NNPP, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
Haka kuma, shugabannin jam’iyyar sun karɓi wasu kungiyoyi biyu da suka sauya sheƙa daga jam’iyyun APC da NNPP.
Me Makinde ya ce kan PDP?
Da yake jawabi ga mahalarta taron, Makinde ya ce yawan mambobin jam’iyyar da suka halarta taron, tare da masu sauya sheƙa, ya nuna karara cewa wadanda ke ikirarin PDP ta mutu sun yi kuskure.
“Zan iya tabbatar muku cewa PDP na nan da ranta, kuma tana da karfi. Duk wanda ke tunanin akasin haka zai yi mamaki fiye da yadda yake zato."
- Gwamna Seyi Makinde
Makinde ya ba 'yan PDP shawara
Ya bukaci shugabanni da mambobin jam’iyyar a fadin yankin da su ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya tare da jajircewa.
Gwamna Makinde ya jaddada muhimmancin karfafa tsarin jam’iyyar a cikin al’umma, mazabu da kananan hukumomi.
“Saboda haka, sakona gare ku shi ne, ku rike al’ummominku, ku rike mazabunku, ku rike kananan hukumominku, komai zai tafi mana daidai."
- Gwamna Seyi Makinde
Makinde ya kuma karfafa wa mambobin jam’iyyar gwiwa da su kasance masu aminci da biyayya, yana mai bayyana kwarin gwiwa kan makomar PDP.

Source: Facebook
PDP na nan daram
A nasa bangaren, yayin da yake maraba da Makinde da sauran shugabannin jam’iyyar, Ladi Adebutu ya ce PDP ta riga ta karyata masu sukar ta, yana mai jaddada cewa jam’iyyar na nan tsintsiya madaurinki daya.
“Mu tsaya daram a cikin PDP. A yanzu muna da tsari tun daga matakin mazabu har zuwa kasa baki daya. Don haka babu abin tsoro."
- Ladi Adebutu
Babban jigo a PDP ya koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai ba PDP shawara kan harkokin siyasa, Emmanuel Enoidem, ya fice daga jam'iyyar.

Kara karanta wannan
Lissafi zai iya canzawa, Tinubu ya shiga ganawa da gwamnan PDP a fadar shugaban kasa
Emmanuel Enoidem wanda ya taba rike mukamin kwamishina a jihar Akwa Ibom ya koma jam'iyyar APC mai mulki.
Enoidem ya gode wa gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, bisa rawar da ya taka wajen sasanta shi da tsohon jagoransa na siyasa kuma shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Asali: Legit.ng

