Abba Ya Rike Akidar Kwankwasiyya Gam duk da Rabuwar da jam'iyyar NNPP

Abba Ya Rike Akidar Kwankwasiyya Gam duk da Rabuwar da jam'iyyar NNPP

  • Gwamnatin Kano ta yi karin haske game da ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar NNPP bayan makonni ana surutu
  • A wani sakon karin bayani da Sunusi Bature D-Tofa ya yi, ya bayyana cewa sauya shekan ba ya nufin barin tsarin Kwankwasiyya
  • Gwamnatin Kano ta jaddada ci gaba da biyayya ga akida da tafarkin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da aka taho a kai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ficewar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi daga jam’iyyar NNPP ba ta nufin an bar tsarin Kwankwasiyya da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta.

Wannan karin bayani ya zo ne awanni kaɗan bayan gwamnatin Kano ta sanar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya fallasa yadda aka zuga Abba kan rabuwa da Kwankwaso

Gwamnatin Kano ta ki rabuwa da Kwankwasiyya
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf a wani taro Hoto: Hon. Alh Sunusi Surajo Kwankwaso
Source: Facebook

A wani sako da hadimin Gwamna, Sanusi Bature D-Tofa, ya wallafa a shafin Facebook, an bayyana karara cewa barin jam’iyya ba ya nufin rabuwa da akida.

Gwamnatin Kano ta yi magana kan barin Kwankwasiyya

A cewarsa, gwamnati da Gwamna Abba Kabir Yusuf na nan daram a kan tsarin Kwankwasiyya, wato akidar siyasa da tafarkin shugabanci da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya assasa.

A cikin sakon, Sanusi Bature ya jaddada cewa har yanzu Gwamna na tare da tsari da akidar siyasar Kwankwasiyya.

A kalamansa:

“Akwai banbanci tsakanin barin jam’iyya da barin akida. Za mu ci gaba da rike akidar Kwankwasiyya daidai gwargwado, domin ita ce tushen tafiyarmu ta siyasa.”

A ranar Juma’a, 23 ga watan Janairu, ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam’iyyar NNPP sakamakon rikice-rikicen shugabanci da dambarwar cikin gida.

Wannan mataki ya jawo cece-kuce da martani daga al’umma, musamman a kafafen sada zumunta, inda mutane ke bayyana ra’ayoyinsu kan makomar siyasar Kano da matsayin Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

"Ba za a ci amana da ni ba:" Kwankwaso ya ajiye mukaminsa a gwamnatin Abba

Martanin jama'a kan matsayar gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa duk da ficewa daga NNPP, ba za a bar tsarin Kwankwasiyya ba.

Jama'a sun yi martani da Abba ya ki barin Kwankwasiyya bayan barin NNPP
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Jama’a da dama sun yi martani ga matsayar gwamnatin Kano na ci gaba da zama a tsarin Kwankwasiyya tare da barin jam’iyyar NNPP.

Umar Bala Halilu ya ce:

“Tsoron Kwankwaso shi ne mafarin hankali.”

Abdullahi Babba Kwaski ya ce:

“Abin da ka shuka, shi za ka girba.”

Mohd Faisal ya ce:

“Ka fi kowa ƙwazo a wannan tafiya, don haka ina tausaya maka wallahi.”

Abu-Hafiz Bin-Uthman Al-Qiruwiy ya ce:

“Haba Honorable, kar ka ba da mu mana! Don mu yadda muka bar NNPP, haka muka ajiye akidar Kwankwasiyya tafi ruwa. Ba mu saba bin jam’iyya fiye da bin shugaba ba a siyasa. Yanzu kam Mai girma Abba Kabir Yusuf shi ne alƙiblarmu, kuma abin koyi ne a cikin kyawawan ayyukan da yake yi wa al’ummar mu Binni da kewaye.”

Kara karanta wannan

Abba Kabir: Buba Galadima ya yi zazzaga kan maciya amanar Kwankwaso

Kwankwaso ya bar gwamantin Abba

A baya, kun ji cewa Mai bai wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, shawara ta musamman kan harkokin siyasa, Sunusi Surajo Kwankwaso, ya yi murabus daga mukaminsa.

Wannan mataki ya biyo bayan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP, yayin da ake ci gaba da jiran sanarwar sabuwar jam’iyyar da zai koma a hukumance.

Rahotanni sun nuna cewa murabus ɗin Sunusi Kwankwaso ya zo ne a daidai lokacin da siyasar jihar Kano ke fuskantar sauye-sauye masu muhimmanci da daukar hankali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng