NNPP: Sunayen 'Yan Majalisar Wakilai da Suka Bar Kwankwaso Suka Bi Abba
- An fitar da jerin sunayen ’yan Majalisar Wakilai daga jihar Kano da suka bi Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen ficewa daga jam’iyyar NNPP
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin kananan hukumomi da masu mukamai ke ci gaba da sanar da ficewarsu daga jam’iyyar
- Shugabar ciyamomin Kano ta tabbatar da ficewarta daga NNPP, yayin da mataimakin gwamnan Kano bai bayyana matsayinsa ba har yanzu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Rikicin cikin gida da ya dabaibaye NNPP a jihar Kano ya dauki sabon salo, bayan fitar da jerin sunayen ’yan Majalisar Tarayya daga jihar da suka bi Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen barin jam’iyyar.
Wannan mataki na zuwa ne a ci gaba da maganganu kan makomar siyasar Kano, musamman dangantakar da ke tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa sunayen 'yan majalisar wakilai da suka bi Abba Kabir Yusuf a shafinsa na Facebook.
A yayin da wasu manyan ’yan jam’iyyar ke sanar da ficewarsu daga NNPP, har yanzu ana jiran bayyana jam’iyyar da za su koma, lamarin da ya kara daukar hankalin jama'a.
'Yan majalisar wakilai 8 sun bar NNPP
A cewar bayanan da aka fitar, ’yan Majalisar Wakilai takwas daga Kano sun bi sahun Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen yin watsi da NNPP.
Wadannan sun hada da Hon. Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe, mai wakiltar Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa, da Hon. Garba Ibrahim Diso daga mazabar Gwale.
Sauran sun hada da Hon. Hassan Shehu Hussain daga Nassarawa, Hon. Idris Dan Kawu daga Kumbotso, da Hon. Muhammad Chiroma Nalaraba mai wakiltar Gezawa da Gabasawa.
Haka kuma akwai Hon. Rabiu Yusuf daga Takai da Sumaila, Hon. Dakta Ghali Mustapha Tijjani daga Albasu, Gaya da Ajingi, da kuma Hon. Barista Muhammad Bello Shehu daga Fagge.
Kananan hukumomin Kano sun bi sahu
Baya ga ’yan majalisa, shugabannin kananan hukumomi da dama a Kano sun sanar da ficewarsu daga NNPP, suna mai cewa sun bi sahun gwamnan jihar.
Shugabar ciyamomin jihar Kano, Hon. Sa'adatu Salisu Abdullahi, ta wallafa sakon fita daga jam'iyyar NNPP a shafinta na Facebook.
A cikin wasikar murabus din, ta bayyana cewa ta yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ne domin bin sahun jagoranta, Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Source: Facebook
Ta ce ta dauki matakin ne bayan nazari, tana mai cewa gwamnan ya taka rawar gani wajen bunkasa Kano da walwalar al’ummarta ta hanyar ayyuka da manufofi masu ma’ana.
Duk da haka, har yanzu mataimakin gwamnan Kano bai fito fili ya sanar da barin NNPP ba kuma ana ci gaba da ganinsa tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Buba Galadima ya gargadi Abba Gida Gida
A wani labarin, mun kawo muku cewa jagora a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya gargadi Abba Kabir Yusuf kan cin amanar Rabiu Kwankwaso.
Buba Galadima ya bayyana cewa tun a 2019 Kwankwaso ya rabu da manyan abokansa na siyasa saboda goyon bayan Abba Kabir.
Ya kara da cewa maciya amana ba su yin nasara a rayuwa, saboda haka idan Abba ya ci amanar Kwankwaso babu shakka zai gani a kwaryarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


