"Ba za a Ci Amana da Ni ba:" Kwankwaso Ya Ajiye Mukaminsa a Gwamnatin Abba
- Sunusi Surajo Kwankwaso ya yi murabus daga mukaminsa na mai ba Gwamnan Kano shawara ta musamman a kan siyasa
- Murabus din ya biyo bayan rahoton ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP, inda ake sa ran zai koma APC
- Alhaji Sunusi Kwankwaso ya jaddada biyayyarsa ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tafiyar Kwankwasiyya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Mai ba Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, shawara ta musamman a kan harkokin siyasa, Sunusi Kwankwaso, ya yi murabus daga mukaminsa.
Wannan ya biyo bayan ficewar Gwamna Abba daga jam’iyyar NNPP, yayin da ake jiran ya sanar da sabuwar jam'iyyar da zai koma.

Source: Facebook
Wannan lamari ya bayyana ne a wani faifan bidiyo da aka saki ranar Juma’a 23 ga watan Janairu, 2026, wanda mai taimaka wa Sunusi a harkokin yada labarai, Saifullahi Hassan, ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Hadimin Gwamnan jihar Kano ya yi murabus
A cikin bidiyon, Sunusi ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan samun rahotanni masu karfi da ke nuna cewa Gwamna Abba Yusuf ya bar NNPP.
Sunusi Kwankwaso a ce ana sa ran gwamnan zai koma jam'iyya mai mulki ta APC a cikin yan kwanaki masu zuwa.
Ya ce tun da farko ya rubuta takardar murabus ya mika, amma ba a karba ta a hukumance ba, lamarin da ya sa ya yanke shawarar fito ya sanar da murbaus dinsa ta bidiyon.
Kwankwaso ya gode wa Gwamnan Kano
Sunusi Kwankwaso ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da aka ba shi na yin aiki tare tsawon kusan shekaru biyu.
A jawabinsa, Sunusi Kwankwaso ya bayyana karara cewa ba zai bi sawun gwamnan ba wajen shiga jam’iyyar APC.
Ya ce biyayyarsa tana nan daram ga jagoran kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma tafiyar Kwankwasiyya baki daya.
A cewarsa, ba zai taba cin amanar Kwankwaso ko akidar da suka dade suna fafutuka a kanta ba.
Ya kara da cewa tsayuwarsa a NNPP ba wai don anfani na kashin kansa ba ne, illa saboda akida, gaskiya, da amana ga mutanen da suka yi imani da tafiyar Kwankwasiyya.
A kalamansa:
“Ba na sayar da kai na, kuma ba za a ci amana da ni ba."
Sunusi Kwankwaso ya yi murabus ne awanni kadan bayan gwamnatin Kano ta sanar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam'iyyar NNPP.
Gargadin Kwankwaso bayan Abba ya bar NNPP
A baya, mun wallafa cewa tsohon 'dan takarar shugaban kasa a NNPP kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi bayani bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bar jam'iyya.
Ya shaida wa magoya baya a gidansa cewa ba zai taba sayar da kansa a siyasa ba, komai irin matsin lamba ko tayin da za a yi masa a tafiyar siyasar kasar nan.
Kwankwaso ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke Kano, jim kadan bayan bullar rahotannin Abba Kabir Yusuf ya bar NNPP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

