Abba Kabir: Buba Galadima Ya Yi Zazzaga kan Maciya Amanar Kwankwaso

Abba Kabir: Buba Galadima Ya Yi Zazzaga kan Maciya Amanar Kwankwaso

  • Buba Galadima ya yi tsokaci kan kalaman Rabiu Musa Kwankwaso da ya yi a gidansa, inda jagoran NNPP ya gargadi maciya amana a siyasa
  • Tsohon dan siyasar ya ce duk wanda ya ci amanar Sanata Kwankwaso, ciki har da Abba Kabir Yusuf, sakamakon hakan zai bayyana a aikinsa
  • A bayanin da ya yi, Buba Galadima ya jaddada cewa Abba ya shafe fiye da shekara 30 tare da tsohon gwamnan a siyasa da harkokin gwamnati

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Dan siyasa kuma jigo a tafiyar Kwankwasiyya, Buba Galadima, ya yi karin haske kan dangantakar da ke tsakanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Ya yi wadannan kalamai ne jim kadan kafin Abba Kabir Yusuf fita daga jam’iyyar NNPP, inda aka tambaye shi kan maganar da Kwankwaso ya yi a gidansa cewa “maciya amana za su gani”.

Kara karanta wannan

"Ba za a ci amana da ni ba:" Kwankwaso ya ajiye mukaminsa a gwamnatin Abba

Rabiu Musa Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf da Buba Galadima
Jagororin NNPP, Rabiu Kwankwaso, Buba Galadima da gwamna Abba Kabir Yusuf. Hoto: Kwankwasiyya Reporters|Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Buba Galadima ya yi ne a wani bidiyo da tashar Trust TV ta wallafa a shafinta na Facebook bayan hira da shi.

Batun 'maciya amanar' Kwankwaso

Da aka tambayi Buba Galadima ko kalaman Kwankwaso kan 'maciya amanarsa' sun shafi Abba Kabir Yusuf kai tsaye, sai ya ce Kwankwaso bai kama suna ba. Amma ya kara da cewa ka’idar siyasa ba ta canzawa.

A cewarsa:

“Idan Abba Kabir Yusuf ya ci amanar Kwankwaso, zai gani a kwaryarsa.”

Buba Galadima ya bayyana cewa wannan magana ba barazana ba ce, illa dai fahimtar sakamakon dabi’ar siyasa da abin da ke faruwa a rayuwa.

A lokacin da ya yi wannan bayani, Abba bai fita daga NNPP ba, yana mai cewa idan har ya yanke shawarar tafiya, ba Kwankwaso yake yaki ba, zai yi fada da ikon Allah ne.

Maganar 'Abba tsaya da kafarka'

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fito ya yi gargadi bayan Gwamna Abba Kabir ya fita daga NNPP

Buba Galadima ya kuma yi tsokaci kan furucin da ake yawan ji na cewa “Abba tsaya da kafarka”. Ya ce idan Abba yana tsaye ne da kafar Kwankwaso, to ba zai iya tsayuwa da kafarsa ba.

Da aka tambaye shi ko hakan na nufin Abba ba zai iya samun gashin kansa a wata jam’iyya ba, musamman APC, Buba Galadima ya ki yin karin bayani, yana mai barin maganar a bude.

Jigo a NNPP, Buba Galadima
Buba Galadima na bayani ga 'yan Kwankwasiyya. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

Tsohuwar alakar Kwankwaso da Gwamna Abba

Buba Galadima ya bayyana cewa Abba Kabir Yusuf ya shafe fiye da shekara 30 tare da Kwankwaso, tun kafin shiga siyasa, a siyasa, da kuma a harkokin gwamnati.

Ya ce Kwankwaso ya sadaukar da abubuwa da dama domin Abba, har ma ya rasa manyan mutane saboda ya zabe shi a matsayin wanda zai zama gwamna.

A cewarsa, zai iya kirga sama da manya 20 da suka rabu da Kwankwaso saboda wannan zabin. Ya kara da cewa a 2019 Abba ne ya ci zabe, amma Allah bai nufa ya zama gwamna ba, inda aka ayyana Abdullahi Ganduje da taimakon Muhammadu Buhari.

Barin NNPP: Kwankwaso ya yi martani

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan fitar gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu jami'an gwamnati daga NNPP.

Kara karanta wannan

An fara: Hadimin Abba ya fita daga Kwankwasiyya, ya magantu kan Kwankwaso

Jagoran NNPP a Najeriya ya bayyana cewa ba yau irin haka ke faruwa a siyasa ba, yana mai kira ga matasa su dage da tallata akidar Kwankwasiyya.

Kwankwaso ya kara da cewa da kudi ya ke fatan samu, da shi ma ya bi tafiyar da mutane ke bi a Najeriya, amma ya tsaya ne domin talakawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng