Kwankwaso Ya Fito Ya Yi Gargadi bayan Gwamna Abba Kabir Ya Fita daga NNPP
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jaddada cewa ba zai taba sadaukar da akidarsa ta siyasa domin kudi ba, yana mai cewa gwagwarmayarsa ta talakawa ce
- Jawabinsa ya zo ne bayan rahotannin ficewar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da wasu shugabanni daga jam’iyyar NNPP, lamarin da ya kara tayar da kura
- Kwankwaso ya bukaci magoya bayansa su fara shiri tun yanzu domin zaben 2027, yana mai gargadin kada a yi sakaci da abin da ke faruwa a Kano a halin yanzu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa ba zai sayar da kansa a siyasa ba.
Kwankwaso ya fadi haka ne a jawabinsa ga magoya bayansa a gidansa da ke Kano, jim kadan bayan bullar rahoton da ke nuna cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da wasu shugabanni, sun fice daga jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan
Tsagin Kwankwaso a NNPP ya yi martani mai zafi kan ficewar Gwamna Abba daga jam'iyya

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi ne a wani sako da hadiminsa, Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Gargadin da Rabiu Kwankwaso ya yi
Da yake jawabi ga magoya bayansa, Kwankwaso ya ce tsawon shekarunsa a siyasa ya nuna cewa burinsa shi ne ‘yantar da talakawan Najeriya daga danniya da zalunci.
Ya ce ba zai sayar da kansa ba yana mai cewa akidarsa ta siyasa ce ke sanya shi tsayuwa daram tare da bayyana cewa da kudi ya ke nema da an saye shi tun tuni.
Kwankwaso ya ce:
'Ba domin wannan akida ba, nima da tuni an saye ni. Nima watakila da na shiga jari hujja."
"Mu cigaba da kokari, mu cigaba da jawo hankalin iyalanmu da abokai da makwabta, da abokan sana'a. Domin samun 'yanci ba abu ne mai sauki ba."
'Za a yi ta ganin cikas iri-iri. Domin ga yadda muke gina wannan akida, wasu kuma abin bai musu daidaiba ba, kokari suke suga sun rusa.
"Ina addu'a Allah ya ba mu rai da lafiya, ya nuna mana lokacin zabe muga yadda za su yi ruwan kuri'a a Kano."
Batun akidar Kwankwasiyya da juriya
Jagoran Kwankwasiyyar ya jaddada cewa abin da ya hada shi da magoya bayansa shi ne manufa daya, ba bukatar abin duniya ba.
Punch ta rahoto ya ce irin sadaukarwar da magoya bayansa suka yi a tsawon lokaci ita ce ke kara masa kwarin gwiwa na ci gaba da gwagwarmaya.

Source: Facebook
Kwankwaso ya yi kira ga mabiyansa da su fara shiri tun yanzu domin zaben shekarar 2027, inda ya yi godiya ga mataimakin gwamnan Kano, Sanata Rufa'i Hanga da sauran mabiya Kwankwasiyya a fadin jihar.
Abba ya fita daga jam'iyyar NNPP
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya fita daga jam'iyyar NNPP da Rabiu Kwankwaso ke jagoranta.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Juma'a, 23 ga Janairun 2026 bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na gwamnatin Kano.
Har yanzu Abba Kabir bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba, duk da cewa hasashe na nuna cewa zai koma APC mai mulki a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
