'Yan Majalisar Tarayya 2 daga Kano Sun Bi Sahun Gwamna Abba, Sun Fice daga NNPP
- Yan Majalisar wakilai na jihar Kano sun fara tura wasikun ficewa daga NNPP jim kadan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bar jam'iyyar
- Dan majalisar Kumbotso, Hon Dankawu Idris da takwaransa na Tofa, Dawakin Tofa da Rimin Gado, Tijjani Abdulkadir Jobe sun fice daga NNPP
- Sun bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne sakamakon rikicin cikin gida da ya hana jam'iyyar NNPP sakat tun daga mazaba har matakin kasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Yan Majalisar wakilan tarayya na jihar Kano sun fara yanke shawara kan ci gaba da zama a jam'iyyar NNPP ko kuma su bi Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Legit Hausa ta gano cewa yan Majalisar tarayya biyu daga Kano sun yanke shawarar bin Abba Gida-Gida, sun mika takardar murabus daga jam'iyyar NNPP a hukumance.

Kara karanta wannan
Abin da aka yi wa tutar NNPP a gidan gwamnatin Kano ya ja hankalin mutane, bidiyo ya fito

Source: Facebook
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, dan majalisa mai wakiltar mazabar Kumbotso a majalisar wakilai, Hon. Dankawu Idris ya fice daga jam'iyyar NNPP.
'Dan Majalisar Kumbotso ya bar NNPP
Dan Majalisar ya tabbatar da haka ne a wata wasika da ya aike wa shugaban NNPP na mazabar Guringawa, a karamar hukumar Kumbotso.
Wasikar ta ce:
"Ni, Hon. Idris Dankawu, zababben dan majalisa mai wakiltar mazabar Kumbotso a Majalisar Wakilai ta Tarayya, na rubuta wannan wasika ne domin sanar da ku ficewa ta daga jam’iyyar NNPP a hukumance.
"Wannan mataki ya biyo bayan rikicin cikin gida da rudanin da ya dabaibaye shugabancin jam’iyyar tun daga matakin mazaba, kananan hukumomi, jiha, har zuwa matakin kasa baki daya.
"Sakamakon haka, ba ni da wani zabi illa na fice daga jam’iyyar domin kare muradin al’ummar da nake wakilta a Kumbotso, da kuma neman sabon tsari da zai ba ni damar ci gaba da gudanar da ayyukana na majalisa yadda ya kamata.
"Ina yi wa shugabancin jam’iyyar NNPP fatan alheri a ayyukansu na nan gaba. Na gode.
Hon. Jobe ya bi sahun Gwamna Abba
Haka zailka, Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe, mamba mai wakiltar Tofa, Dawakin Tofa da Rimin Gado a Majalisar wakilai ya mika takardar ficewarsa daga NNPP.
A takardar da wani Hon. Abdullahi ya wallafa a shafinsa na X yau Juma'a, dan Majalisar ya ce ya dauki matakin fita daga NNPP ne saboda rigingimun da suka dabaibaye ta.

Source: Twitter
Hon. Jobe ya ce:
"Ina rokon ku da ku karbi wannan wasika a matsayin sanarwar ficewa ta daga jam’iyyar NNPP, wadda za ta fara aiki nan take.
"Wannan mataki ya zama dole ne sakamakon rabuwar kai a cikin jam’iyya da kuma shari’un kotu da suka ki ci suka ki cinyewa, tun daga matakin jiha har zuwa matakin kasa, wadanda ke kawo cikas ga zaman lafiya da hadin kai a NNPP."
An cire tutar NNPP a gidan gwamnatin Kano
A wani labarin, kun ji cewa an cire tutar NNPP daga fadar gwamnatin jihar Kano bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da ficewarsa daga jam'iyya.
Wani faifan bidiyo ya nuna yadda wani jami'i ya nannade tutar NNPP, sannan ya dauke ta ya yi waje da ita a gidan gwamnatin da ke cikin birnin Kano.
Bayan wannan bidiyo ya fara yawo, 'yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan cire tutar NNPP da kuma ficewar Gwamna Abba daga jam'iyya.
Asali: Legit.ng

