Rikicin Rivers; Fadar Shugaban Kasa Ta Sace Gwiwoyin Wike kan Takaddamarsa da Fubara

Rikicin Rivers; Fadar Shugaban Kasa Ta Sace Gwiwoyin Wike kan Takaddamarsa da Fubara

  • Ana ci gaba da muhawara kan rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa dangane da siyasar jihar Rivers mai arzikin mai
  • Fadar shugaban kasa ta fito ta yi tsokaci kan rikicin siyasar wanda ya sa alaka ta yi tsami tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike
  • Hadimin Shugaba Tinubu ya bayyana cewa shugaban kasar yana kan matsayar da Nentawe Yilwatda ya dauka dangane da matsayin Gwamna Fubara

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Daniel Bwala, mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara ta musamman kan yada manufofi, ya yi magana kan rikicin siyasar jihar Rivers.

Daniel Bwala ya ce Shugaba Bola Tinubu ya gamsu da matsayar shugaban jam'iyyar APC na kasa, Nentawe Yilwatda, kan tsarin shugabanci a jihar Rivers.

Fadar shugaban kasa ta yi goyi bayan Gwamna Fubara
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da Nyesom Ezenwo Wike Hoto: @GovWike, @SimFubaraKSC
Source: Facebook

Hadimin shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Hard Copy' na tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi halin da yake ciki kan gudanar da mulkin Najeriya

Ana yunkurin tsige Gwamna Fubara

Maganar Bwala na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dokokin Jihar Rivers ke ci gaba da yunkurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara .

Haka kuma an yi musayar kalamai tsakanin Gwamna Fubara da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.

Fubara ya samu goyon baya

Daniel Bwala ya ce dole ne a bar gwamna ya gudanar da ayyukansa ba tare da katsalandan ko matsin lamba ba.

Ya ƙara da cewa tasirin siyasar Wike a jihar Rivers ya tsaya ne kawai a cikin jam’iyyar PDP.

“Ina goyon bayan abin da shugaban APC na ƙasa ya faɗa cewa a jihar Rivers, Gwamna Fubara shi ne jagoran APC. Wike ba mamba ne na APC ba, don haka ba zai iya magana da yawun jam’iyyar ba."
"Ana iya kallon Wike a matsayin jagora a cikin PDP a jihar Rivers, kasancewarsa tsohon gwamna, amma jagoran APC a jihar Rivers shi ne Gwamna Fubara.”

Kara karanta wannan

Lissafi zai iya canzawa, Tinubu ya shiga ganawa da gwamnan PDP a fadar shugaban kasa

- Daniel Bwala

Tinubu na goyon bayan matsayar shugaban APC

Bwala ya ce matsayar Shugaba Tinubu ta yi daidai da dokokin cikin gida na jam’iyya da kuma ƙa’idojin dimokuraɗiyya.

“Abin da shugaban jam’iyya ya faɗa shi ne matsayar da shugaban kasa ya tsaya a kai, domin yana girmama dokokin jam’iyya. Shugaban ƙasa yana mutunta doka da bin ƙa’ida, kuma jam’iyya za ta ci gaba da yin hakan."

- Daniel Bwala

Daniel Bwala ya ce Fubara ne jagoran APC a Rivers
Daniel Bwala, hadimin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @BwalaDaniel
Source: Twitter

Me aka ce kan Wike?

Bwala ya kuma taɓo batun koke-koken da ake yi kan tasirin Wike a gwamnatin tarayya, inda ya ce nadin mukamai ba ya fifita muradun kasa.

“Mun ji mutane na cewa kasancewar Wike mamba a majalisar ministoci yana samun wasu fa’idoji."
"An riga an saka wa Wike yadda ya kamata. Shugaban kasa yana son ya saka wa mutane da alheri, amma ba zai taɓa yin abin da zai cutar da muradun Najeriya ba. Shugaba Bola Tinubu yana da sassauci, amma idan ka ketare iyaka, za ka sani.”

Kara karanta wannan

An gama magana: Shugaba Tinubu ya sharewa gwamnan Kano fagen shiga APC

- Daniel Bwala

Shirin tsige Fubara ya gamu da cikas

A wani labarin kuma, kun ji cewa yunkurin 'yan majalisar dokokin jihar River na tsige Gwamna Siminalayi Fubara ya gamu da cikas.

Babban alkalin jihar Rivers, Mai shari'a Simeon Amadi ya ƙi amincewa da buƙatar majalisar kan kafa kwamiti domin binciken Gwamna Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, bisa zargin aikata manyan laifuffuka.

Mai shari’a Amadi ya sanar da shugaban majalisar dokokin cewa doka ta hana shi daukar irin wannan mataki, saboda akwai umarnin kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng