APC: Gwamna Abba Ya Saka Rana, Zai Tattara Ya Bar Kwankwaso a Jam'iyyar NNPP

APC: Gwamna Abba Ya Saka Rana, Zai Tattara Ya Bar Kwankwaso a Jam'iyyar NNPP

  • Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya sake saka wata sabuwar rana ta sauya sheka daga NNPP zuwa APC mai mulkin Najeriya
  • An d Gwamnan ya saka sabon lokacin ne bayan an shade tsawon kwanaki ana daga sauya shekar saboda batutuwa da dama
  • Rahotanni sun bayyana cewa bayan cimma matsaya kan jadawalin barin jam'iyyarsa, an saka ranar karban katin APC

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya tsayar da wata rana ta daban domin sauya sheka daga jam’iyyarsa ta NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu cimma wannan matsaya ne bayan jerin dage wa da jinkirin da aka samu game da batun.

Gwamnan Kano ya saka sabuwar ranar sauya sheka
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yana jawabi a gaban taro Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Rahoton da ya kebanta ga jaridar Daily Nigerian ya tabbatar da cewa Gwamnan ya sanar da wannan rana ne bayan taron sirri da tsakar dare na ranar Alhamis, 22 ga watan Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya tashi tawaga, zai sanar da Kwankwaso shirinsa na koma wa APC

Gwamna Abba zai bar NNPP zuwa APC

Rahoton ya bayyana cewa an sanya jerin lokutan barin NNPP, sanar da koma wa APC da karban katin jam'iyya bayan taron sirri da ya gudana a tsakanin Gwamna da ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Wani da ya halarci taron kuma ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa gwamnan ya sanya ranar Asabar, 24 ga watan Janairu, 2026 domin yin murabus daga NNPP.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma sanya ranar Lahadi 25 ga watan Janairu, 2026 domin sanar da shigarsa APC, sannan Litinin 26 ga watan Janairu, 2026 domin karbar katin jam’iyya.

Ya kuma sanar da ’yan majalisar cewa ya kulla yarjejeniya da hedikwatar jam’iyyar ta kasa kan 60% na kujeru da tasiri a tsarin jam’iyyar.

Abba ya magantu game da Kwankwaso

Gwamnan ya kara da cewa za a kafa wani kwamitin da zai tsara hanyoyi da ka’idoji na yadda zai samu rinjaye mai yawa a babban taron jam’iyyar da ke tafe.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna ya sha alwashi, zai ceto mutum sama da 170 da 'yan ta'adda suka sace

Abba Gida-Gida ya ce bisa bukatar ’yan majalisa, ya gana da Shugaban kasa domin kokarin shawo kan Rabi'u Musa Kwankwaso ya mara masa baya ta hanyar bin sa APC.

Ko da yake an shirya ganawar Shugaban kasa da Kwankwaso tun da fari a ranar Talata, majiyoyi sun ce watakila an soke taron.

Kwankwaso ba zai bi Abba zuwa APC ba
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Wani hali Kwankwaso yake ciki?

An kuma gano cewa Kwankwaso ya yanke shawarar ba zai shiga APC ba, yayin da tattaunawar kawance da tsohon dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi.

Rahotanni sun nuna cewa wannan yunkuri na kawance na iya sauya taswirar siyasa a matakin kasa, musamman a Arewacin Najeriya, inda tasirin Kwankwaso ke da karfi a tsakanin matasa da masu rajin sauyi.

Duk da bangarorin ba su ce komai ba a hukumance, rahoton ya nuna akwai yiwuwra a ja Kwankwaso zuwa ADC domin su hada kai da Peter Obi a jam'iyyar hadakar.

Hadimin Abba ya bar Kwankwasiyya

A baya, mun wallafa cewa Salisu Yahaya Hotoro, wanda ke daga cikin hadiman Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

APC ta gaji da jiran Abba ya sauya sheka, an fara yi wa jama'a rajista

Hotoro wanda ya taba bayyana Kwankwasiyya a matsayin gida, ce shawarar ficewarsa ba ta zo da sauki ba, amma ta zama dole duba da sabon yanayin siyasar da jihar Kano ke ciki.

Ya bayyana cewa shiga sabon yanayi na siyasa ya sa ya sake nazarin matsayinsa, tare da yanke shawarar bin abin da ya ga ya fi dacewa da muradunsa da kuma makomar aikinsa na siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng