Bayan Ganawa da Tinubu, Gwamna Makinde Ya Yi Magana kan Ficewa daga PDP zuwa APC
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya sanya labule da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Alhamis, 22 ga watan Janairun 2026
- Seyi Makinde ya amsa tambayoyi daga wajen manema labarai kan yiwuwar sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki
- Babban 'dan siyasar kuma babba a PDP na daga cikin sauran 'yan kalilan din gwamnonin da suka rage a jam'iyyar mai adawa a Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi magana kan batun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC ko wata jam'iyya daban.
Gwamna Makinde ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa zai fice daga PDP, inda ya bayyana cewa yana nan daram kuma yana jin daɗin zamansa a jam’iyyar adawa.

Source: Facebook
Seyi Makinde ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da tashar NTA ta sanya a shafinta na X a ranar Alhamis, 22 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan
Lissafi zai iya canzawa, Tinubu ya shiga ganawa da gwamnan PDP a fadar shugaban kasa
Gwamna Makinde ya amsa tambaya kan barin PDP
Gwamna Makinde ya yi jawabin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Alhamis, a yayin ziyararsa zuwa Aso Rock Villa.
A cikin bidiyon, gwamnan ya amsa tambaya kan makomarsa ta siyasa da kuma yiwuwar ficewa daga jam'iyyar PDP.
“A’a, a’a, a’a. Ina jin daɗi kwarai a PDP. Haka kuma, akwai lokuta a kasar nan da ake buƙatar haɗin kai tsakanin jam’iyyun siyasa."
"Ba wai APC kaɗai za ta yi magana ba, ko PDP kaɗai ba, sai dai a zauna a duba wace hanya ce ta fi dacewa domin amfanin kasa baki ɗaya."
“Idan an kai wannan mataki, dole ne kowa ya ba da tasa gudunmawar."
- Gwamna Seyi Makinde
Tinubu ya gana da Makinde, Mutfwang
Tun da farko Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da tarurruka daban-daban da Gwamna Makinde da kuma gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan
APC ta shirya, an ji muhimman dabaru 4 da za su iya sa Tinubu ya lashe zaben 2027
Gwamnonin biyu sun isa fadar Aso Rock Villa lokuta daban-daban, inda Mutfwang ya iso da misalin karfe 3:00 na rana, yayin da Makinde ya biyo baya da misalin 3:30 na rana.
Wadannan tarurruka na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar siyasa yayin da manyan ’yan siyasa ke shirin tunkarar zaɓen gama-gari na 2027.

Source: Twitter
Ana hasashen Makinde zai fito takara a 2027
Makinde, wanda mamba ne na PDP, na daga cikin ’yan kaɗan daga cikin gwamnoni da suka rage a jam’iyyar, duk da yawan sauya sheƙa da ake yi zuwa APC mai mulki.
Haka kuma, ana ganin gwamnan na da burin tsayawa takarar shugaban kasa, kuma yana kokarin shirya kansa domin neman tikitin PDP a zaɓen 2027.
A gefe guda kuma, gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC kwanan nan, inda ya shiga jerin manyan ’yan adawa da suka koma jam’iyya mai mulki.
An kai karar Makinde gaban EFCC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Kungiyar HEDA ta kai karar Gwamna Seyi Makinde gaban hukumar EFCC kan zargin karkatar da Naira biliyan 30 na tallafin Bodija.
Ƙungiyar tana tuhumar gwamnatin jihar da rashin bayyana gaskiyar yadda aka batar da Naira biliyan 30 da gwamnatin tarayya ta bayar bayan fashewar da ta auku a Bodija.
Ta bayyana damuwarta cewa Naira biliyan 4.5 kawai aka yi amfani da su wajen biyan diyya, yayin da sauran Naira biliyan 30 suka yi batan dabo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
