2027: Atiku Ya Fara Bambami tun Yanzu, Ya Soki Sanatoci kan Taba Dokar Zabe a Majalisa

2027: Atiku Ya Fara Bambami tun Yanzu, Ya Soki Sanatoci kan Taba Dokar Zabe a Majalisa

  • Tsohon 'dan takarar Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zargi Majalisar Dattawa da hannu a kokarin jawo cikas ga shirin babban zabe mai zuwa
  • Ya zargi Sanatoci da jinkirta gyaran Dokar Zaɓe ta 2022, musamman yayin da aka sa rai za a yi amfani da canje-canjen a zaben shekarar 2027
  • A cewar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, giɓin dokar ne ya jawo maguɗin zaɓen 2023 da wahalar shari’a da aka rika fama da shi bayan zaben

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi Majalisar Dattawan Najeriya da jinkirta ƙoƙarin gyara dokar zaɓe ta 2022.

A zargin da Atiku Abubakar ya yi, ya ce Sanatocin sun jawo jinkirin ne da gangan, inda ya yi gargaɗin cewa irin wannan jinkiri na iya lalata sahihanci da amincin zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Abubakar Malami ya yi magana game da makamai da DSS ta gano a 'gidansa' na Kebbi

Atiku Abubakar ya hango abin da zai jawo cikas ga zaben 2026
Tsohon dan takarar Shugaban Kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Wannan koke na tsohon dan takarar Shugaban kasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, 22 ga watan Janairu, 2026.

Atiku Abubakar ya dura a kan Sanatoci

A cikin sanarwar, Atiku ya bayyana cewa kura-kurai da ke cikin dokar zaɓe ta 2022 da jinkirin gyara su na daga cikin manyan abubuwan da suka jawo koma-baya ga zaɓen 2023.

Ya ce waɗannan giɓi ne suka buɗe ƙofa ga maguɗin zaɓe muraran, tare da jawo kalubale ga masu shigar da ƙorafi a gaban kotu.

Atiku ya ce:

“Babban koma-baya ga zaɓen 2023 ita ce giɓin da ke cikin dokar zaɓe ta 2022, wanda ya bai wa masu maguɗi damar yin a bayyane."

Ya jaddada cewa wajibi ne a ɗauki matakin gaggawa na doka domin kauce wa maimaita irin waɗannan matsaloli a zaɓuka masu zuwa, musamman zaɓen 2027.

Atiku na son a gyara dokar zaɓen Najeriya

Kara karanta wannan

Makwabtan Fatima da aka kashe da yaranta 6 a Kano sun fusata rundunar 'yan sanda

A cewar Atiku Abubakar, idan ana son gyara kura-kuran da aka yi a zaɓen 2023, to dole ne a sake duba da sabunta dokar da za ta jagoranci zaɓen 2027 da na gaba.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP ya kuma zargi Majalisar Dattawa da jawo cikas wajen tabbatar da gyaran dokar zaben.

Atiku ya zargi Sanatoci da jawo tsaiko a gyaran dokar zabe
Wasu daga cikin Sanatoci a zaman majalisa Hoto: The Nigerian Senate
Source: UGC

Ya ce a halin da ake ciki yanzu, a bayyane ya ke cewa Majalisar Dattawa ta ƙuduri aniyar hana wucewar gyare-gyaren da ake so a yi wa dokar.

Atiku ya yi gargaɗin cewa rashin gyara dokar kafin zaɓen 2027 zai zama kamar shiri ne da gangan na lalata tsarin dimokuraɗiyya da sahihancin zaɓe.

Ya ce amincin zaɓen 2027 ya ta’allaka ne da yadda Majalisar Dattawa za ta yi gaggawa wajen kammala wannan muhimmin kudiri.

A cewarsa, ya zama wajibi Majalisar ta kammala gyare-gyaren tare da tabbatar da cewa sabuwar dokar ce za ta jagoranci gudanar da zaɓen 2027.

Kungiyar tallata Atiku ta kori Abba

A baya, mun wallafa cewa Musa Bakari, wanda ya kafa kuma ke jagorantar ƙungiyar Atiku Haske, ya sanar da korar Abba Atiku Abubakar daga ƙungiyar bayan sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Takarar 2027: Yadda ake son tada rikici a ADC da matakin da Atiku ya dauka

Rahotanni sun ce bayan sauya sheƙar, Abba Atiku ya umarci magoya bayansa da ke ƙarƙashin tsarin siyasar da yake jagoranta su koma APC tare da fara tattara goyon baya ga manufar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ƙungiyar Atiku Haske ta ce matakin korar ya zama dole ne saboda sabon matsayinsa na siyasa, wanda bai yi daidai da manufofi da burin ƙungiyar ba, sannan ba da ko sisinsa ake gudanar da ƙungiyar ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng