‘Bala’in da Ya Tunkaro APC kan Jita Jitar Sauya Shettima a Matsayin Mataimaki’
- Wata ƙungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta gargaɗi jam’iyya da kada ta cire Kashim Shettima daga tikitin Bola Tinubu a zaɓen 2027
- Ta ce cire Shettima zai zama babban kuskuren siyasa da zai iya lalata shirin sake zaɓen Shugaba Tinubu idan ya nemi ya zarce
- Masoyan na APC a Arewa ta Tsakiya sun jaddada cewa sauya tikitin Musulmi-Musulmi zai ƙarfafa adawa maimakon kawo nasara
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ƙungiyar APC ta yankin Arewa ta Tsakiya ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi na cire Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.
Ana ta yada jita-jitar cewa za a sauya Shettima daga matsayin abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓen shekarar 2027.

Source: Twitter
Wannan matsayi na ƙungiyar ya fito ne a cikin wata sanarwa da shugabanta, Alhaji Saleh Zazzaga, ya fitar, bayan jita-jitar cewa wasu jiga-jigan jam’iyya na son a sauya Shettima, cewar Punch.
An gargadi Tinubu kan sauya Shettima
Ƙungiyar ta bayyana cewa duk wani yunkuri na sauya Shettima zai zama mummunan kuskuren siyasa da ka iya jefa jam’iyyar APC cikin matsala.
Ta ce sauya Shettima zai zama bala’i ga jam’iyyar, tare da barazana ga burin Tinubu na sake lashe zaɓe.
Ƙungiyar ta jaddada cewa yankin Arewa ta Tsakiya ba ya neman kujerar mataimakin shugaban ƙasa, domin burinsu shi ne fafatawa da kujerar shugaban ƙasa a 2031 bayan wa’adin Tinubu.
Ta ce:
"Akwai babbar barazana wajen sauya tikitin da ya kawo nasara. Muna ƙin amincewa gaba ɗaya da kiran ko shirye-shiryen cire Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, daga matsayin abokin takarar Tinubu a zaɓe mai zuwa."

Source: Twitter
Gargadin 'yan APC ga jam'iyya mai mulki
Ta kuma gargaɗi jam’iyya da kada ta shigar da addini cikin lissafin siyasa, tana mai cewa a halin yanzu babu ɗan Arewa Kirista da ke da cikakken tasiri, karɓuwa da tsari na siyasa da zai ƙara wa Tinubu ƙarfi.
A cewar ƙungiyar, sauya tikitin Musulmi-Musulmi zai ƙarfafa jam’iyyun adawa ne kawai a zaɓen 2027.
Sanarwar ta ce sauya tikitin da ya kai ga nasara a 2023 na ɗauke da haɗari sosai, tare da jaddada cewa kiran cire Shettima kuskure ne babba.
Ƙungiyar ta zargi masu wannan kira da rashin son ganin Tinubu ya sake lashe zaɓe, tana mai cewa ba su mara masa baya tun a 2023 ba, kuma ba za su yi hakan a 2027 ba.
Ta ƙara da cewa ko da APC ta sauya Shettima, hakan ba zai hana masu goyon bayan Peter Obi ko jam’iyyar ADC kaɗa masa ƙuri’a ba, cewar Vanguard.
“Idan ka duba sosai, za ka lura cewa a shekarar 2023 yawancin al’ummominsu sun kaɗa ƙuri’a ne ga Peter Obi na jam’iyyar LP.
“Yanzu idan Peter Obi ya sake fitowa a 2027 a ƙarƙashin tutar ADC, wace irin tabbaci ake da shi cewa za su kaɗa wa Tinubu ƙuri’a ko da ya sauke Shettima ya maye gurbinsa da Kirista? Hakan ba zai faru ba.”
- Cewar sanarwar
A ƙarshe, ƙungiyar ta shawarci Shugaba Tinubu da ya ci gaba da rike Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa domin ƙarfafa damar APC a zaɓen 2027.
Rashin hoton Shettima ya rikita taron APC
A wani labarin, rigima ta kaure kan rashin sanya hoton Sanata Kashim Shettima a taron masu ruwa da tsakin APC na Arewa maso Gabas.
Kakakin Majalisar dokokin jihar Borno, Rt. Hon. Abdulkarim Lawal ya nuna bacin ransa a wurin taron, wanda ke gudana a Maiduguri.
Mahalarta taron sun amince da maganganun da kakakin Majalisar ya yi, wanda ya ce masu shirya taron ba su yi adalci ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


