APC Ta Shirya, An Ji Muhimman Dabaru 4 da Za Su Iya Sa Tinubu Ya Lashe Zaben 2027

APC Ta Shirya, An Ji Muhimman Dabaru 4 da Za Su Iya Sa Tinubu Ya Lashe Zaben 2027

  • Jam'iyyar APC na ci gaba da lalubo dabarun da za su ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu nasara karo na biyu a zaben 2027
  • Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce matasan Najeriya ke yafiyar da jam'iyyar, wanda hakan alamu ne na nasara
  • Ya ce APC na kara bunkasa ta hanyar samun karin gwamnoni, 'yan Majalisar tarayya da na jihohi, 'yan kasuwa da manoma a fadin Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana kan turbar sake lashe zabe a karo na biyu.

Nentawe ya bayyana cewa sun shirya wasu dabaru wadanda yake da yakinin cewa za su sake cicciba Bola Tinubu zuwa nasara a zaben 2027 da ke tafe, idan har ya shiga takara.

Kara karanta wannan

2027: Alamu sun nuna wasu ministoci da hadimai za su rasa mukamansu a gwamnatin APC

Shugaban APC.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Yilwatda Nentawe da wasu jiga-jigai a taron matasan Arewa maso Yamma Hoto: @OfficialAPCNIG
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce ya bayyana hakan ne a daren ranar Talata a Abuja, yayin taron matasan APC na shiyyar Arewa maso Yamma wanda Karamin Ministan Ayyuka, Bello Goronyo, ya shirya.

Dabaru 4 da APC ta shiryawa zaben 2027

Yayin da yake bayyana dabarun da ya yi amanna za su ba Tinubu nasara, Yilwatda ya ambaci karuwar goyon bayan matasa, nasarorin manufofin gwamnati, fadada jam’iyya, da amfani da sahihan bayanai wajen tara magoya baya.

Manyan shugabannin jam’iyyar da suka halarci taron sun bayyana cewa, sabanin abin da 'yan adawa ke fada, nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a aikace suna kara dawo da kwarin gwiwar jama’a.

A cewarsu, 'yan Najeriya sun kara gamsuwa da cewa gwamnatin za ta iya ceto kasar daga koma-bayan da ta fuskanta shekaru da dama zuwa ga bunkasa da kwanciyar hankali.

Jiga-jigan jam'iyyar da suka halarci taron APC

Daga cikin manyan baki da suka halarci taron akwai Karamin Ministan Raya Yankuna, Uba Maigari Ahmadu; Karamar Ministar Abuja, Dr. Mariya Mahmud.

Kara karanta wannan

'Dalilin da zai sanya Peter Obi ya fice daga jam'iyyar ADC kafin zaben 2027'

Haka zalika rahoto ya ce an ga Karamin Ministan Jin Kai da Rage Radadin Talauci, Dr. Tanko Sununu wanda shugaban kasa ya canza wa ma'aikata a 2025.

Sauran sun hada da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa; Shugaban Matasan APC na Kasa, Dayo Israel; da mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa (PCC) na shiyyar Arewa maso Yamma.

"APC ta yi fice a nahiyar Afirka" - Nentawe

Shugaban APC, Farfesa Nentawe ya ce kokarin Shugaba Tinubu da kuma karuwar goyon bayan da yake samu a matakin mazabu ya sa APC ta zama “jam’iyyar siyasa mafi girma a Afirka."

“Kowace rana muna ci gaba da karbar gwamnoni, muna karbar mambobin Majalisar Dokoki ta Kasa. Mu na karbar 'yan kasuwa mata, manoma, da dalibai,” in ji shi.

Ya yi nuni da cewa matasan Najeriya ne ke kara karfafa APC, yana mai jaddada cewa “jam’iyyar ta matasa ce.”

Shugaban APC na kasa.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Yilwatda Nentawe a wurin taron masu ruwa da tsaki na jihar Filato Hoto: @Nentawe1
Source: Twitter

Ya kara da cewa kashi 48 na mambobin APC a Arewa maso Yamma shekarunsu na tsakanin 18 zuwa 35, yayin da a matakin kasa, mambobin da shekarunsu ke tsakanin 18 zuwa 49 sun kai kashi 83, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Kara karanta wannan

APC ta ware matsayin da za ta ba Kwankwaso idan ya sauya sheka tare da Gwamna Abba

APC za ta yi rowan mukamai bayan 2027

A wani labarin, kun ji cewa shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce 'yan jam'iyya da suka mata wahala kadai za a ba mukamai bayan zaben 2027.

Farfesa Nentawe ya jaddada cewa shugabanci abu ne na siyasa, don haka dole ne wadanda aka nada su goyi bayan jam’iyyar da ta kawo su kan mulki.

Ya kara da cewa manufofin gwamnati su ne alkawuran da ta yi a lokacin kamfe, kuma ya zama dole wadanda za su jagoranci aiwatar da su, su kare su, su bayyana su, kuma su tallata su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262