APC Ta Gaji da Jiran Abba Ya Sauya Sheka, An Fara Yi wa Jama'a Rajista

APC Ta Gaji da Jiran Abba Ya Sauya Sheka, An Fara Yi wa Jama'a Rajista

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta fara rijistar mambobinta ta yanar gizo bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke jan kafa wajen sauya sheka
  • Rahotanni a baya sun bayyana cewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a dage fara rajista har sai Gwamna ya koma APC
  • Amma da alama ana samun jan kafa, domin kawo yanzu, Gwamna Abba Kabir Yusuf bai sanar da sauya sheka ko sa ranar da zai koma APC ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – APC reshen jihar Kano ta fara rijistar 'ya'yanta ta yanar gizo, a daidai lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke ci gaba da jinkirta sanar da ranar da zai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar.

Kara karanta wannan

APC ta ware matsayin da za ta ba Kwankwaso idan ya sauya sheka tare da Gwamna Abba

Tun da farko, shugabannin APC na Kano sun sanya ranar 15 ga Janairu a matsayin ranar fara rijista ta yanar gizo a jihar, sai dai daga baya aka dage ranar saboda sa rai da sauya shekar Abba.s

APC ta fara rajistar 'ya'yanta ana jiran Gwamna ya sauya sheka
Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Hoto: Abdullahi Abbas/Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wata majiya da ta san yadda lamarin ke gudana ta shaida wa jaridar Daily Nigerian cewa, da Gwamnan ya lura APC a Kano na ci gaba da shirin rijista, sai ya kai karar lamarin ga Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.

Yadda aka dakatar da rajistar jam'iyyar APC

A cewar majiyar, Mataimakin Shugaban Kasa ya umarci shugaban jam’iyyar APC na kasa, Yilwatda Nentawe, tare da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, da su dakata su jira gwamnan ya sauya sheƙa kafin a kaddamar da rijistar.

Jam’iyyar mai mulki ta yi hasashen cewa Gwamna Abba zai sauya sheƙa ne a ranar 5 ga Janairu, 2026 wace ta yi daidai da ranar haihuwarsa.

Sai dai daga baya aka sauya ranar zuwa 12 ga Janairu, saboda yawancin shugabannin APC a jihar suna hutun shekara ko aikin Umrah.

Sai aka sake dage ranar sanarwar zuwa 16 ga Janairu, 2026 inda aka ce za a yi ta ne bayan taron Majalisar Zartarwa na Jiha da aka gudanar a Abuja tare da manema labarai.

Kara karanta wannan

APC ta fayyace wanda zai zama jagora a Kano tsakanin Gwamna Abba da Ganduje

An jinkirta sauya shekar Gwamna Abba zuwa APC na tsawon lokuta
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Amma abin mamaki, bayan taron, ba a yi sanarwar sauya sheƙar ko maganar cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai bar jam'iyyarsa ta NNPP ba.

Bayan dagewar ranar 16 ga Janairu, 2026 an ce gwamnan ya sake sanya ranar 20 ga Janairu, 2026 — wato kwana guda bayan ganawarsa da Shugaban Kasa, Bola Tinubu.

Wani jagoran jam’iyya da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar cewa gwamnan ya roki shugabancin jam’iyyar na kasa da a ba shi “ƙarin lokaci domin faɗaɗa tuntubar jama'a”.

Sai dai duk abin da yake faruwa, gwamnatin Kano ba ta taba sanar da batun sauya-shekar Abba ba.

Jam'iyyar APC ta gaji da jiran Abba

Majiyoyin sun bayyana cewa a halin yanzu, reshen APC na Kano ya riga ya kaddamar da kwamitin rijistar 'ya'yanta ta kafar yanar gizo ganin har yanzu Gwamnan ya ki sauya sheka.

Alhaji Rabiu Suleiman-Bichi, Shugaban hukumar kula da kogin Hadejia-Jama’are, da Baffa Babba-Dan’agundi, ne ke jagorantar kwamitin.

Kara karanta wannan

Aikin gama ya gama, Shugaba Tinubu ya shiga ganawa da gwamnan Kano a Abuja

Ko da yake an ce an tanadi katin zama lamba daya wato 001 ga gwamnan a mazabarsa ta Diso da ke Karamar Hukumar Gwale, rijistar ta fara gudana a fadin jihar Kano.

Dalilin jinkirin sauya shekar Gwamna - APC

A wani labarin, kun ji cewa shirin sauya shekar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyar adawa ta NNPP zuwa mai mulkin Najeriya waro APC ya samu tsaiko.

Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa jinkirin ya samo asali ne daga rashin cimma matsaya tsakanin bangarorin biyu, musamman kan batun neman tikitin takara kai tsaye a zaben gwamna

Rahotanni sun nuna cewa APC ba ta amince da sharadin da ake zargin gwamnan ya gabatar na samun damar tsayawa takara kai tsaye ba tare da shiga zabukan fitar da gwani ba,

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng