An Fara: Hadimin Abba Ya Fita daga Kwankwasiyya, Ya Magantu kan Kwankwaso

An Fara: Hadimin Abba Ya Fita daga Kwankwasiyya, Ya Magantu kan Kwankwaso

  • Hadimin Abba Kabir Yusuf, Salisu Yahaya Hotoro ya bayyana ficewarsa daga tafiyar Rabiu Musa Kwankwaso bayan ce-ce-ku-ce na siyasa
  • Ya ce fitarsa ta samo asali ne daga ra’ayinsa na kansa da kuma dambarwar siyasa da ke gudana tsakanin Abba Kabir Yusuf da Kwankwaso
  • Hotoro ya jaddada cewa har yanzu yana bayyana cewa shi ɗan talaka ne, amma kuma ya yanke shawarar barin tafiyar Kwankwasiyya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Salisu Yahaya Hotoro da ke daga cikin hadiman Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya da Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta.

Hotoro ya bayyana haka ne bayan wani tsohon rubutu da ya taba wallafawa a shafinsa na Facebook ya sake bayyana, inda ya nuna kansa a matsayin ɗan talaka mai ra’ayin Kwankwasiyya a wancan lokacin.

Kara karanta wannan

Kujerar Hajji, sabon gida da wasu kyaututtuka 3 da Gwamna Abba ya yi waijin Fatima

Salisu Yahaya Hotoro
Hadimin gwamnan Kano da ya fita a Kwankwasiyya. Hoto: Salisu Yahaya Hotoro
Source: Facebook

A wata hira da aka yi da Salisu Yahaya Hotoro kuma ya wallafa a Facebook, ya bayyana cewa ya shafe shekaru yana tafiyar Kwankwasiyya amma komai ya zo karshe.

Bayanin ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da dambarwar siyasa tsakanin Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a Kano.

Abin da ya faru da hadimin Abba Kabir

A cewar Salisu Yahaya Hotoro, batun ficewarsa daga Kwankwasiyya ta samo asali daga wani tsohon rubutu, lokacin da ya bayyana cewa shi ɗan talaka ne kuma ya tashi a gidan talakawa kuma dan Kwankwasiyya.

Ya ce a wancan lokaci ya bayyana kansa a matsayin ɗan Kwankwasiyya, sai dai abubuwa sun canza, musamman da aka shiga sabon yanayi na siyasa a Kano.

Salisu Yahaya Hotoro ya kara da cewa yanzu da ake ganin ya karkata wajen Abba Kabir Yusuf maimakon Rabiu Kwankwaso sai aka rika tuna masa rubutun da ya yi a baya.

Kara karanta wannan

'Yadda alakar Abba da Kwankwaso take bayan jita jitar zai bar NNPP zuwa APC'

Salisu Hotoro ya fita daga Kwankwasiyya

Salisu Yahaya Hotoro ya bayyana cewa bai musanta asalinsa na talaka ba, yana mai cewa har yanzu yana tsayawa kan cewa shi ɗan talaka ne kuma a gidan talakawa ya tashi.

Sai dai ya ce bayan dambarwar siyasa da ta ɓarke tsakanin Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso, ya yanke shawarar goyon bayan Abba Kabir Yusuf, lamarin da ya jawo kalubale daga wasu da ke ganin ya bar Kwankwasiyya.

Ya ce shekaru sama da 18 ya shafe yana tallata Rabiu Musa Kwankwaso kuma kamata ya yi a gode masa bisa hakan da ya yi.

A cewarsa, duk da irin gudunmawar da ya bayar a baya wajen yaɗa manufofin Kwankwaso, a yanzu ya zaɓi goyon bayan Abba Kabir Yusuf, yana masa biyayya a duk inda yake a siyasa.

Gwamna Abba Kabir tare da Rabiu Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso tare da Abba Kabir Yusuf. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Ya ce bai kamata a kalle shi a matsayin mai laifi ba, domin lokacin da ya shiga Kwankwasiyya ba a tilasta masa ba, da kansa ya yanke shawarar shiga.

Kara karanta wannan

Shigar Abba APC: Kwankwaso ya fitar da sanarwa ga yan Kwankwasiyya

Haka kuma ya ce kamar yadda ya shiga da kansa, haka nan ya yanke shawarar fita da kansa, don haka bai dace a tuhume shi ko a matsa masa lamba ba saboda ra’ayinsa na siyasa.

Makomar Kwankwasiyya a siyasar Kano

A wani labarin, mun kawo muku cewa mai magana da yawun gwamnan Kano ya yi karin bayani game da sauya shekar Abba Kabir Yusuf.

Sanusi Bature D-Tofa ya bayyana cewa ana tattaunawa da jam'iyyu amma har yanzu gwamnan bai dauki matakin sauya sheka ba.

Hadimin gwamnan ya kara da cewa Abba Kabir yana tafiya a kan tsarin Kwankwasiyya a yanzu, kuma babu abin da zai shafi tafiyar daga baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng