Akwai Matsala: Yunkurin Jawo Kwankwaso zuwa APC Ya Fara Gamuwa da Cikas a Kano

Akwai Matsala: Yunkurin Jawo Kwankwaso zuwa APC Ya Fara Gamuwa da Cikas a Kano

  • Ana rade-radin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin zama da jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso domin shawo kansa ya dawo APC
  • Wasu daga cikin masu ruwa da tsakin APC a jihar Kano sun nuna rashin amincewarsa da yunkurin jawo Sanata Kwankwaso zuwa jam'iyyar
  • Sai dai sun amince Gwamna Abba ya shiga APC amma ba tare da Kwankwaso ba, saboda suna hangen zai iya danne su a siyasar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Wasu jiga-jigan APC daga Kano sun gargadi fadar shugaban kasa kan illar abin da suka kira “auren dole” a yunkurin da ake yi na ganin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da ubangidansa, Rabiu Musa Kwankwaso, sun koma jam’iyyar.

Wannan gargadi na zuwa ne sakamakon rashin jin dadi da wasu masu ruwa da tsaki na APC a Kano suka nuna game da yiwuwar dawowar Kwankwaso APC.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, an kara zuga Gwamna Abba kan rabuwa da Kwankwaso

Kwankwaso.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa galibin masu ruwa da tsakin na APC a Kano ba su da matsala da sauya shekar Gwamna Abba daga NNPP zuwa APC.

Yunkurin jawo Kwankwaso ya rikita APC

To amma wasu daga cikinsu ba su maraba da dawowar Kwankwaso APC, inda suka nuna cewa barin tsohon ministan ya dawo APC na iya zama tamkar “auren dole," a siyasar Kano.

Sai dai kuma, an samu labarin cewa fadar shugaban kasa ta dage lallai sai Gwamna Abba ya dawo tare da ubangidansa don tabbatar da cewa an murkushe jam’iyyar NNPP gaba daya a jihar.

Wannan takaddama na zuwa ne yayin da rahotanni ke nuna cewa tsohon gwamnan na Kano zai gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu nan ba da dadewa ba don tattauna batun sauya shekar.

Kwankwaso na shirin ganawa da Tinubu

Wata majiya da ke kusa da tafiyar Kwankwasiyya ta tabbatar da cewa: “Jagoranmu (Kwankwaaso) ya shirya tsaf don ganawa da Shugaban Kasa a kowane lokaci daga yanzu.”

Kara karanta wannan

An gama magana: Shugaba Tinubu ya sharewa gwamnan Kano fagen shiga APC

A baya, an ji Kwankwaso yana cewa ba zai koma jam’iyya mai mulki ba har sai ya tabbatar da abin da shi da magoya bayansa za su samu.

Amma wata majiya mai tushe a APC ta ce Shugaba Tinubu a yanzu ya shirya tattaunawa kai-tsaye da Kwankwaso kan sharuddan da zai dawo.

Jiga-jigan APC a Kano sun hango matsala

Wannan lamari ya jefa damuwa a tsakanin mambobin APC a Kano, inda wasu jiga-jigai suka nuna sun fi son Abba ya dawo shi kadai ba tare da Kwankwaso ba.

A cewarsu, suna fargabar Kwankwaso zai mamaye ikon jam’iyyar APC a Kano ya kuma gurgunta tasirin wadanda suke ciki, idan ya sauya sheka.

Kwankwaao da Bola Tinubu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwanwkaso Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Wani jigo da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa jaridar Nigerian Tribune a Abuja cewa:

“Akwai tsoron cewa ba za a yi wa tsofaffin mambobin APC adalci ba idan aka mika ragamar ga Kwankwaso.”

APC ta budewa Kwankwaso kofa

A wani rahoton, kun ji cewa APC reshen jihar Kano ta ce a shirye take ta karbi jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso idan ya amince zai shiga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

APC ta sace gwiwar gwamnonin da ke tururuwar sauya sheka gabanin zaben 2027

Shugaban APC na jihar, Abdullahi Abbas ya ce za su karbi Rabiu Kwankwaso idan ya sauya sheka tare da mai girma gwamna Abba , Kabir Yusuf, kuma zai shiga cikin iyayen jam'iyya.

Abdullahi ya tabbatar da cewa Kwankwaso zai iya zama daya daga cikin iyayen APC a Kano idan ya sauya sheka amma ba zai yiwu ya zama shi ne jagora ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262