Anyanwu: Kotu Ta Kawo Karshen Dambarwar PDP kan Kujerar Sakataren Jam'iyya
- Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da Samuel Anyanwu ya shigar domin tabbatar da shi a matsayin sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa
- Lauyan Anyanwu ya shaida wa kotu cewa wa’adin aikinsa ya ƙare tun a watan Disambar 2025, lamarin da ya sa shari’ar ta zama mara amfani
- Rikicin shugabanci a PDP ya ƙara fito da rabuwar kai tsakanin ɓangarorin da Nyesom Wike da kuma gwamnonin jam’iyyar ke mara wa baya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da Samuel Anyanwu ya shigar, inda yake neman a amince da shi a matsayin sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa.
Mai shari’a Mohammed Umar, wanda ke jagorantar shari’ar, ya yanke hukuncin ne a ranar Talata 20 ga watan Janairu, 2026.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wannan na zuwa ne bayan da lauyan Anyanwu, U. C. Njemanze-Aku, ya shaida wa kotu cewa wa’adin aikinsa a matsayin sakataren PDP ya ƙare tun a watan Disambar 2025.
PDP: Kotu ta kori karar Sanata Sam Anyanwu
Daily Post ta ruwaito cewa a ƙarar da aka yi wa lamba FHC/ABJ/CS/254/2025, Anyanwu ya roƙi kotu ta hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) da kuma Umar Damagum kan aiki da wata wasika marar sa hannunsa.
Lokacin da aka kira shari’ar domin sauraro a ranar Talata, lauyan Anyanwu ya bayyana cewa an riga an kammala batun sabida haka bai dace a ci gaba da shari'ar ba.

Source: Twitter
Ya ce:
“Don tabbatar da adalci, ina roƙon kotu ta ba ni damar janye wannan ƙara domin a ceci lokacin kotu.”
Lauyan INEC, Akintayo Balogun, ya ce bai kamata a shigar da ƙarar tun farko ba, inda ya roƙi kotu ta yi watsi da ita tare da ɗora tara ta N1m a kan batun.
Lauyan Damagum, M. O. Akpan, shi ma ya mara wa wannan roƙo baya. Bayan sauraron dukkannin ɓangarori, mai shari’a Umar ya yi watsi da ƙarar ba tare da ɗora wata tara ba.

Kara karanta wannan
Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci
Yadda jam'iyyar PDP ta shiga rikici
An dade ana rikici a kan matsayin sakataren PDP na kasa, inda Samuel Anyanwu, Sunday Udeh-Okoye da Setonji Koshoedo ke ikirarin suke da kujerar.
A watan Disamba, wani ɓangare na PDP da Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, ke mara wa baya, ya rusa kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) tare da kafa kwamitin rikon ƙwarya.
An naɗa Abdulrahman Mohammed a matsayin shugaba, yayin da aka sanya Anyanwu a matsayin sakataren jam'iyyar PDP na kasa.
Sai dai a watan Nuwamba, wani ɓangare na jam’iyyar da gwamnonin PDP ke goyon baya, ciki har da Bala Mohammed na Bauchi da Seyi Makinde na Oyo, sun gudanar da taro inda suka zaɓi sabbin shugabanni.
PDP ta yi sabon sakataren jam'iyya
A baya, kun samu labarin cewa
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
