Daga Kujeru 41 zuwa 0: Yadda LP Ta Rasa duka 'Yan Majalisa bayan Nasara a 2023

Daga Kujeru 41 zuwa 0: Yadda LP Ta Rasa duka 'Yan Majalisa bayan Nasara a 2023

Jam'iyyar LP ta ba da mamaki matuka a zaben da ya gabata a Najeriya, inda ta samu nasarar lashe kujerun sanatoci, yan Majalisar wakilai da na jihohi da dama a shekarar 2023.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

'Daya daga cikin babbar nasarar da jam'iyyar ta samu shi ne kafa gwamnati a jihar Abia da ke Kudu maso Gabashin Najeriya bayan naarar dan takararta na gwamna, Alex Otti.

Jam'iyyar LP.
Tutar jam'iyyar LP da aka kafa a jihar Abia Hoto: @LabourNG
Source: Twitter

A wani rahoto da This Day ta tattara, LP ta samu nasarar lashe kujerun sanatoci shida da 'yan Majaliaar wakilai 35, lamarin da ya sa ta shiga Majalisar Tarayya da manyan fata bayan zaɓen 2023.

Amma cikin ƙasa da shekara uku, jam’iyyar ta rasa kusan dukkan kujerun majalisar tarayya sakamakon sauya sheƙa, rikice-rikicen cikin gida da matsin siyasa.

A zaɓen 2023, LP ta yi abin da mutane da dama ba su zata ba, inda ta samu kujeru a Majalisa ta 10 musamman sakamakon tasirin Peter Obi da kuma goyon bayan matasa musamman 'yan Obidient.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kwankwaso, Gawuna yayin ziyara ga Haruna Bashir da aka hallaka iyalinsa

Jam’iyyar ta zama ta uku mafi karfi a siyasar ƙasa bayan APC da PDP, lamarin da ya girgiza manyan jam’iyyun a Najeriya.

A wannan rahoton, mun tattaro muku yadda LP ta rasa duka sanatocin da ta samu a zaben 2023, da kusan duka 'yan Majalisar wakilai da dalilin da suka jawo mata haka a kasa da wa'adin zango daya.

Nasarorin sa LP ta samu a zaben 2023

Jam'iyyar LP ta ba da mamaki a babban zaben da ya gabata, inda ta yi abin da galibin 'yan Najeriya da masana ba su yi zato ba, kama daga kafa gwamnatin jiha da lashe kujeru yan Majalisa da dama.

PR Nigeria ta ce LP ta samu nasarori masu yawa a zaben 2023, kuma daya daga cikin nasarar da ta fi daukar hankali ita ce matsayin da jam'iyyar ta kare a sakamakon zaben shugaban kasa.

Jagoran LP kuma tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya zo na uku a zaben shugaban kasar da ya gudana, wanda Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara a 2023.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya fara bambami tun yanzu, ya soki Sanatoci kan taba dokar zabe a majalisa

Ana ganin Peter Obi ne ya jagoranci LP ta lashe zaben gwamna a jihar Abia, ta samu kujerun sanatoci shida da 'yan Majalisar wakilai 35.

Bugu da kari, LP ta lashe kujerun majalisar jihohi da dama a Abia, Enugu, Edo, Anambra da wasu jihohi musamman a Kudu maso Gabashin Najeriya.

Me ya raba LP da kujerun Majalisarta?

Sai dai daga watan Yuni, 2023 da aka rantsar da Majalisar tarayya ta 10 zuwa yanzu, jam'iyyar LP ta rasa duka kujerun sanatocin da ta samu da kisan duka 'yan Majalisar Wakilai.

Hakan ya faru sakamakon abubuwa da dama da suka faru a cikin jam'iyyar da kuma yanayin siyasar kasar, wanda aka fara zargin ana neman maida Najeriya mulkin jam'iyya daya.

1. Rikicin cikin gida a LP

'Daya daga cikin manyan dalilan da suka nakasa LP shi ne rikicin cikin gida, wanda ya raba jam'iyyar har zuwa gida biyu, kamar yadda jaridar Guardian ta kawo.

Wanna rikici ya fi zafi ne tsakanin tsagin Julius Abure, wanda ke ayyana kansa a matsayin shugaban LP na kasa da bangaren kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin Nenadi Usman.

Kara karanta wannan

APC ta gaji da jiran Abba ya sauya sheka, an fara yi wa jama'a rajista

Tsagin Nenadi Usman na samun goyon bayan Gwamna Alex Otti na jihar Abia, hatta Peter Obi na tare da wannan bangare kafin ya bar LP zuwa ADC.

Galibin sanatoci da 'yan Majalisar wakilai sun kafa hujja da rikicin da ya damu LP a matsayin dalilinsu na ficewa daga jam'iyyar.

2. Guguwar sauya sheka

Majalisar dattawa da majalisar wakilai na cikin bangarorin da guguwar sauya sheka ta taba a Najeriya, inda mambobin jam'iyyun adawa irinsu LP, PDP, APGA da sauransu suka rika sauya sheka.

Galibi dai 'yan Majalisar sun fi yawan ficewa daga jam'iyyun adawa zuwa APC mai mulki, lamarin da wasu suka fara kallo da yunkurin maida Najeriya mulkin jam'iyya daya.

Masana da masu sharhi kan harkokin siyasa da 'yan adawa sun soki tururuwar da yan majalisa, gwamnoni da yan siyasa suka rika yi zuwa APC, suna mai cewa hakan illa ce ga dimukradiyya, in ji rahoton Bussiness Day.

Wannan lamari na cikin abubuwan da suka raba LP da wasu daga cikin 'yan majalisar da take da su a Majaliaar tarayya ta 10.

Peter Obi.
Tutar jam'iyyar LP da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

3. Tasirin ficewar Peter Obi daga LP

Kara karanta wannan

Kotu ta hukunta makiyayan da suka saki dabbobi a gonakin manoma

A ranar Laraba, 31 ga watan Disamba, 2025, tsohon dan takarar shugaban kasa, Mista Oeter Obi ya sauya sheka zuwa jam'iyyar hadaka, ADC a hukumance.

The Cable ta rahoto cewa a wani taro da ya gudanar a jihar Enugu, Peter Obi ya bayyana cewa sun shirya tsaf domin tunkarar zaben 2027.

Obi ya ce:

“Mun kammala wannan shekara da fatan cewa a 2026 za mu fara tafiyar ceto al'ummarmu, Za mu yaki maguɗin zaɓe ta kowace hanya da doka ta halatta a 2027.”

Wannan mataki da Peter Obi ya dauka wanda shi da magoya bayansa 'yan Obidiemt suka jagoranci LP ta samu nasara a 2023, ya sake ruguza jam'iyyar.

Ragowar sanatocin LP a Majalisar dattawa tare da wasu 'yan Majalisar Wakilai sun bi Obi zuwa ADC, lamarin da ya kara durkusar da shirin jam'iyya gabanin zaben 2027.

Mece ce mafita ga jam'iyyar LP?

Babban abin da ke ciwa jam'iyya LP shi ne rikicin shugabanci a matakin kasa, wanda ya kai gaban kotu.

A rahoton Tribune Nigeria, ranar Alhamis da ta gabata, babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yanke hukuncin cewa wa'adin Abure ya kare a matsayin shugaban LP na kasa.

Kara karanta wannan

'Dalilin da zai sanya Peter Obi ya fice daga jam'iyyar ADC kafin zaben 2027'

Kotun ta umarci INEC da ta amince da kwamitin rikon kwarya karkashin jagoranci Nenadi Usman, to sai dai duk da wannan hukunci tsagin Abure ya lashi takobin daukaka kara.

Ana ganin duk da LP ta rasa Peter Obi da 'yan Majalisarta, za ta iya farfadowa idan ta warware rikicin shugabanci tsakanin bangaren Abure da Nenadi Usman.

Julius Abure da Nenadi Usman.
Shugabannin bangarorin LP biyu, Julius Abure da Nenadi Usman Hoto: @LabourNG
Source: Facebook

LP ta hango nasarar Peter Obi a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar LP ta sake tayar da muhawara kan bukatar hadin kan jam’iyyun adawa don kifar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Bangaren jam’iyyar da ke goyon bayan Peter Obi da gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa dole yan adawa su kulla hadaka idan suna son karbar mulki a 2027.

Bisa haka, LP ta roki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya hakura ya marawa Obi baya, domin shi ne kadai zai iya buga APC da kasa a akwatun zabe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262