Atiku Ko Obi? An Fadi Wanda Zai Tarwatsa ADC idan Aka ba Shi Takara a 2027
- Tsohon Mai bai wa shugaban kasa shawara, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi magana game da abin da zai yi saurin ruguza ADC
- Baba-Ahmed ya ce jam’iyyar ADC za ta shiga rikici idan Atiku Abubakar ya samu tikitin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa
- Tsohon hadimin shugaban kasan ya ce Atiku na da karfin samun tikitin ADC, amma hakan zai sa ‘yan takara da magoya baya da dama su fice
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi hasashen wargajewar ADC.
Baba-Ahmed ya bayyana cewa jam’iyyar ADC za ta shiga babbar matsala idan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya samu tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Source: Facebook
An hango matsalar da ta tunkaro ADC
Baba-Ahmed ya bayyana haka ne yayin wata hira a shirin Politics Today na tashar Channels Television, inda ya yi magana kan yanayin siyasa a cikin jam’iyyar ADC da kuma burin manyan ‘yan siyasar da ke cikinta.
A cewarsa, Atiku Abubakar na da cikakken matsayi da karfi da za su ba shi damar zama dan takarar ADC idan jam’iyyar ta gudanar da babban taronta na kasa, lamarin da ya ce zai haddasa ficewar ‘yan takara da magoya baya masu rashin jin dadi.
Ya ce:
“Idan ADC ta je babban taro, kuma lallai za ta je domin shi ne abin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ke so, babu shakka zai samu tikitin.
“Bayan haka, mutane da dama za su fice daga jam’iyyar, domin yawancin wadanda ke cikinta suna can ne ne saboda buri daya, neman tikitin takarar.”

Source: UGC
Abin da Baba-Ahmed ya hango a ADC
Baba-Ahmed ya bayyana cewa ADC a halin yanzu ta tattaro manyan ‘yan siyasa masu karfi, inda bukatunsu da burinsu za su yi karo da juna da zarar aka fara tantance dan takarar shugaban kasa.
Har ila yau, ya tabo batun tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, inda ya ce salon siyasar Obi bai dace da fafatawar zaben fidda gwani ba.

Kara karanta wannan
Harin tikitin ADC ya kara zafi, tsohon Minista ya ayyana shirin neman shugaban kasa a 2027
Ya ce:
“Daya daga cikin dalilan da ya sa Peter Obi ke cewa ‘ban zo neman mataimaki ba, ban zo taron fitar da gwani ba, na zo ne domin rike tutar jam’iyyar,’ shi ne saboda yana da mutane da da farko suna binsa a hankali.
“Yanzu kuma suna gaya masa cewa ya shiga layi, domin ba shi kadai ke da buri a wannan jam’iyyar ba.”
Baba-Ahmed ya ce Peter Obi ya saba da a zabe shi kai tsaye a matsayin dan takara ba tare da fafatawa da wasu ba.
A karshe, tsohon mai bai wa shugaban kasa shawarar ya ce sakamakon babban taron jam’iyyar ADC na iya girgiza hadakar jam’iyyar baki daya.
An shawarci Atiku ya hakura da takara
An ji cewa Hakeem Baba-Ahmed ya shawarci Atiku Abubakar da ya hakura da neman shugabancin Najeriya, ya zama uban al'umma don ci gaban ƙasa.
Baba-Ahmed ya ce ya kamata Atiku ya zama gwarzon dimokuraɗiyya a matsayinsa na jigon PDP kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa.
Ya kuma buƙaci Atiku da ya mai da hankali kan samar da sababbin shugabanni, masu jini a jika, wadanda za su mulki Najeriya a madadin APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
