Gwamnatin Kano Ta Fadi Makomar Kwankwasiyya Abba na Shirin Shiga APC

Gwamnatin Kano Ta Fadi Makomar Kwankwasiyya Abba na Shirin Shiga APC

  • Gwamnatin jihar Kano ta ce har yanzu ba a yanke matsaya kan rade-radin sauya shekar gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC ba
  • Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce ganawar da aka yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ta shafi siyasa ba
  • Ya ce tattaunawar siyasa na gudana tsakanin jam’iyyu daban-daban, ya kuma yi karin haske kan makomar tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa har zuwa yanzu babu wata matsaya da aka yanke kan yiwuwar sauya shekar gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, duk da karuwar tattaunawar siyasa.

Hasashen sauya shekar ya kara daukar hankali ne musamman bayan ganawar ta gudana a boye tsakanin Abba Kabir Yusuf da shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

'Yadda alakar Abba da Kwankwaso take bayan jita jitar zai bar NNPP zuwa APC'

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf na bayani. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Bayani kan hakan ya fito ne daga bakin mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa yayin hira da ya yi da tashar Channels TV.

Ganawar da Abba ya yi da Tinubu

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya jaddada cewa ganawar gwamna Abba Kabir Yusuf da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ta da alaka da sauya sheka ko wata tattaunawar jam’iyya.

Ya ce gwamnan ya yi amfani da damar ne wajen gabatar wa shugaban kasa halin tsaro da jihar Kano ke ciki, musamman a kananan hukumomin da ke makwabtaka da jihohin Katsina da Kaduna, inda hare-haren ‘yan bindiga ke kara ta’azzara.

A cewarsa, gwamnan ya bukaci karin hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro na tarayya da tsarin tsaron jihar Kano, ciki har da rundunar tsaron al’umma, domin dakile barazanar da ke kunno kai.

Rade-radin sauya shekar Abba

Da yake martani kan rade-radin cewa ganawar Abuja alama ce ta shirin sauya sheka zuwa APC, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce irin wannan mataki ba ya faruwa cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Tinubu zai gana da Kwankwaso bayan zama da Gwamna Abba

Ya bayyana cewa sauya sheka na bukatar la’akari da dokoki, kundin tsarin mulki da kuma yanayin siyasa, yana mai cewa a halin yanzu ana tattaunawa ne kawai ba tare da cimma matsaya ba.

Mai magana da yawun gwamnan Kano
Sanusi Bature da ke magana da yawun gwamnan Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: UGC

A cewarsa, tattaunawar siyasa da 'yan NNPP ke yi ta shafi jam’iyyu da dama ciki har da APC, ADC da LP, lamarin da ya saba gani musamman idan ana gab da manyan zabuka.

Matsayin Kwankwasiyya a siyasar Kano

Sanusi Bature ya amince cewa akwai kalubale a cikin jam’iyyar NNPP, amma ya jaddada cewa tafarkin Kwankwasiyya ya fi kowace jam’iyya karfi.

Daily Trust ta wallafa cewa ya ce Kwankwasiyya ba jam’iyya ba ce, tafarki ne da akida da ke hade magoya baya a fadin jam’iyyu daban-daban.

Ya kuma karyata zargin cewa ana tilasta wa gwamna yin wani zabi na siyasa, yana mai cewa Abba Kabir Yusuf na ci gaba da mai da hankali kan cika alkawurran da ya dauka ga al’ummar Kano a wa’adinsa na mulki daga 2023 zuwa 2027.

Kwankwaso ya yabi 'yan Kwankwasiyya

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fitar da sanarwa da matasa masu akidar Kwankwasiyya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Alfarmar da Gwamna Abba Kabir ya nema yayin ganawa da Tinubu a Abuja

A sanarwar da ya fitar, Sanata Kwankwaso ya yaba wa matasan bisa yadda suke kare akidar Kwankwasiyya a kafafen sada zumunta.

Ya yi bayanin ne a daidai lokacin da ake musayar yawu tsakanin 'yan Kwankwasiyya ana tsaka da rade-radin cewa Abba Kabir Yusuf zai sauya sheka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng