2027: PDP Ta Fadi Yankin da Za Ta ba Tikiti, Ta Magantu kan Takarar Jonathan

2027: PDP Ta Fadi Yankin da Za Ta ba Tikiti, Ta Magantu kan Takarar Jonathan

  • Jam’iyyar PDP ta yi magana game da yankin da za ta takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027 da ke tafe
  • PDP ta bayyana cewa tikitin takarar shugabancin kasa na 2027 a bude yake ga duk ‘yan Najeriya daga Kudancin kasar
  • Shugaban PDP, Tanimu Turaki ya ce jam’iyyar ta yanke shawarar mika tikitin Kudu, inda ya jaddada cewa zaben dan takara zai kasance a bude

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyar PDP karkashin jagorancin tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Tanimu Turaki (SAN), ta magantu kan tikiti a zaben 2027.

PDP ta bayyana cewa tikitin takarar shugabancin kasa a zaben 2027 a bude yake ga duk ‘yan Najeriya daga Kudancin kasar nan da suka cancanta.

PDP ta yi magana game da tikitin zaben shugaban kasa a 2027
Shugaban jam'iyyar PDP, Kabiru Tanimu Turaki. Hoto: Peoples Democratic Party, PDP.
Source: Facebook

PDP ta bude tikitinta ga kowa a Kudu

Tanimu Turaki, wanda ke jagorantar bangaren PDP a halin yanzu, ya bayyana hakan ne a Abuja a daren Talata 20 ga watan Janairun 2026, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Harin tikitin ADC ya kara zafi, tsohon Minista ya ayyana shirin neman shugaban kasa a 2027

Ya fadi hakan ne jim kadan bayan ya jagoranci mambobin Kwamitin Gudanarwa (NWC) zuwa ziyarar girmamawa ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Namadi Sambo.

Jam’iyyar ta ce duk wanda ya fito daga Kudancin Najeriya, kuma ya cika dukkan sharudda na da damar tsayawa takara a karkashin PDP, ciki har da Goodluck Jonathan.

Turaki ya yi wannan bayani ne yayin da ake tambayarsa ko Jonathan ya nuna sha’awar karbar tikitin PDP ko kuma ya sanar da jam’iyyar aniyarsa ta tsayawa takara a 2027?.

Jonathan zai iya yin takara a PDP
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Twitter

'Jonathan zai iya neman takara a PDP'

Turaki ya bayyana cewa Goodluck Jonathan da duk wani dan Kudancin Najeriya na da cikakken ikon neman tikitin jam’iyyar, muddin ya cancanta.

Sai dai Turaki ya kara da cewa jam’iyyar ta riga ta san wasu da ba za a bari su tsaya takara ba, amma ya ki bayyana sunayensu.

A cewarsa:

“Mun yanke shawarar mika tikitin shugaban kasa na PDP zuwa Kudancin kasar nan. A halin yanzu, ba mu san wanda zai zama dan takararmu ba, duk da cewa mun san wadanda ba za su zama ‘yan takara ba.

Kara karanta wannan

'Ka yi hattara,' An fadawa Tinubu abin da zai faru idan ya sauya Shettima a 2027

“Tsarin zai kasance a bude, mai gaskiya, mai adalci da daidaito, domin bai wa kowa damar takara ba tare da fifiko ba.
“Don haka, duk wanda yake mamba a PDP daga Kudancin Najeriya yana da ‘yancin tsayawa takara, kuma ‘yan Najeriya su ne za su yanke hukuncin wanda zai zama dan takararmu.”

Turaki, tare da mambobin NWC, kwamitin amintattu (BoT), dattawa da wasu daga cikin wadanda suka kafa PDP, sun ce sun ziyarci Namadi Sambo ne domin gabatar masa da sabbin shugabannin jam’iyyar da aka zaba a babban taron Ibadan da aka gudanar a ranar 15 ga Nuwamban 2025.

A cewarsa, Namadi Sambo ya nuna farin ciki da ziyartar, inda ya ba su shawarwari da jagoranci kan yadda za su ci gaba da karfafa jam’iyyar, cewar The Guardian.

Fasto ya yi hasashen takarar Jonathan a 2027

An ji cewa Fasto Elijah Ayodele ya yi magana kan yadda za a lallashi Atiku Abubakar ya janye neman takararsa ta shugaban kasa a zaben 2027.

Ya bayyana cewa kungiyoyin kasa da kasa da manyan ‘yan siyasar Najeriya za su mara wa wannan shiri baya domin cire Bola Ahmed Tinubu.

Limamin ya gargadi cewa Amurka, karkashin Donald Trump, za ta zama babbar barazana ga mulkin Tinubu idan bai dauki mataki ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.