Ana Wata Ga Wata: Shugaba Tinubu Zai Gana da Kwankwaso a Abuja, An Samu Bayanai
- Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai karbi bakuncin jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a fadar shugaban kasa yau Talata
- Majiyoyi masu karfi sun tabbatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taka rawa a shirya wannan zama tsakanin Kwankwaso da Tinubu
- Wannan dai na zuwa ne awanni 24 bayan Shugaba Tinubu ya gana da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf kan wasu muhimman batutuwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - A wani sauyi da aka samu a dambarar siyasar Kano, rahotanni sun nuna cewa jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso zai gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Majiyoyi daga Kano sun nuna cewa Tinubu ya shirya wata muhimmiyar da ganawa Kwankwaso nan ba da jimawa ba a fadar shugaban kasa.

Source: Twitter
Majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin sun shaida wa jaridar Politics Digest cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya taka rawa wajen shirya ganawar Kwankwaso da Tinubu.
Abba ya yiwa Tinubu maganar Kwankwaso
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan Shugaba Tinubu ya gana da Gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A cewar majiyoyi, ganawar Abba da Tinubu ta mayar da hankali ne kan sanar da shugaban kasa sharuddan da Kwankwaso ya gindaya na shiga jam'iyyar APC mai mulki.
Wata majiya ta shaida wa Daily Nigerian cewa Abba ya nemi shugaban kasa ya yi magana da Kwankwaso domin shawo kansa ya shiga APC saboda duk rokon da ya masa ya ki amincewa.
Tinubu ya shirya ganawa da Kwankwaso
Wani babban jigo a APC a Arewa maso Yamma ya tabbatar da cewa an tsara ganawa tsakanin Shugaba Tinubu da Sanata Kwankwaso a yammacin yau Talata.
"Shugaban kasa yana son fadada karfinsa a siyasa, ana sa ran taron a yammacin yau, kuma tattaunawar za ta fi mayar da hankali kan zaman lafiyar kasa, hadin kan siyasa, da kuma yadda za a fuskanci 2027."
Ana ganin dai wannan cigaba na kara rura wutar jita-jita kan makomar jam’iyyar NNPP da kuma tafiyar Kwankwasiyya.
Yayin da bangaren Abba ke cikin murna bayan nasarar ganawarsa da Shugaban Kasa, har yanzu ba a tantance ko Kwankwaso da Abba suna shirin ficewa daga NNPP ne tare, ko kuma kowa yana neman hanyarsa ne ta daban.
Masu sharhi kan siyasa sun ce duk wani yunkuri na hadewar Kwankwasiyya da APC zai haifar da gagarumin sauyi a siyasar Najeriya.
Yanzu dai ana kyautata zaton ganawar Tinubu da Kwankwaso ita ce za ta tantance ko Gwamna Abba zai koma APC shi kadai, ko kuma gaba dayan tafiyar Kwankwasiyya za ta nade tabarmarta ta koma APC.
Asali: Legit.ng

