Abba: Jam'iyyar APC Ta Yi Bayani game da Hana Tikitin Takara Kai Tsaye
- Jam’iyyar APC ta yi ƙarin haske kan matsayarta game da hana gwamnoni masu sauya sheka samun tikitin takara kai tsaye a zaɓen 2027
- APC ta shaida wa Legit cewa duk da wannan matsaya, gwamnoni ba sa rasa tagomashi a jam’iyyar, musamman idan sun koma cikinta
- Jam’iyyar ta ce zaɓen fitar da gwani na 2027 zai bi turbar dimokiraɗiyya, amma Gwamnoni masu sauya sheka za su caɓa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –Jam’iyyar APC ta yi ƙarin haske game da matsayar da ta ɗauka kan hana gwamnoni masu sauya sheka samun tikitin takara kai tsaye a zaɓuka masu zuwa.
Sakataren yaɗa labaran APC na Kano, Ahmed S. Aruwa, ya bayyana wa Legit cewa wannan matsaya ba tana nufin cewa gwamnoni ba za su samu tagomashi ko matsayi na musamman a cikin jam’iyyar ba.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa APC ta ce za ta tafiyar da zaɓen fitar da gwani na shekarar 2027 bisa tsarin dimokiraɗiyya, inda kowa zai samu damar tsayawa takarar Gwamna da sauran mukamai.
APC ta nanata kalaman Shugaban jam’iyya
Sakataren yaɗa labaran APC na Kano, Ahmed S. Aruwa, ya bayyana cewa tsarin jam’iyyar APC na girmama gwamna a jiharsa, saboda haka Gwamna Abba Kabir Yusuf zai kasance jagora a jihar Kano idan har ya sauya sheka zuwa APC.
A kalaman Aruwa, jam’iyyar APC tana da manufofi da tsare-tsare da kuma ƙa’idoji da ke jagorantar ayyukanta tun daga ƙasa har zuwa matakin jiha.
Ya ce:
“A cikin ƙa’idojin jam’iyyar APC, duk lokacin da gwamna ya shigo jam’iyyar ko kuma idan ya zama gwamna a karkashin tutar APC, shi ne ke jagorantar jam’iyyar a jiharsa.”
Ya ƙara da cewa:
“Shi ne ake kira 001. A fannin shugabanci da kuma a gwamnatance, shi ne na ɗaya. Kamar yadda Shugaban ƙasa yake lamba ɗaya a matakin ƙasa, haka nan gwamna yake jagora a duk abin da ya shafi jam’iyyar a jiharsa.”
Aruwa ya jaddada cewa saboda haka, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne zai zama jagoran jam’iyyar APC a Kano da zarar ya shigo cikinta, kamar yadda tsarin jam’iyyar ya tanada.
Gwamna zai samu tikitin sake takara a APC
A ƙarin bayani da ya yi kan batun hana gwamnoni tikitin takara kai tsaye, Aruwa ya ce a aikace yana da matuƙar wahala gwamna ya sha kaye a zaɓen fitar da gwani.

Source: Facebook
Ya ce:
“Da fari dai, gwamna idan ma ka ce za ka tsaya takara da shi, abu ne mai wahalar gaske. Ba na cewa ba za a iya ba, amma yana da wahala ƙwarai a kayar da gwamna.”
A cewarsa:
“Duk wani tsari da ya shafi jam’iyya, galibi yana ƙarƙashin ikon gwamna ne, saboda matsayinsa da tasirinsa a cikin jam’iyyar.”
Ya ƙara da cewa ko APC ta ce za a ba da tikitin takara kai tsaye ko kuma ba za a ba da shi ba, shi abin da ya fahimta shi ne an yi shiru ne a kan batun domin a bar al’amura su bi tsarin jam’iyya. Aruwa ya bayyana cewa duk gwamnan da zai koma APC dole ne ya zauna da mutanensa, ya tsara makomarsa da tsare-tsarensa, saboda haka maganar hana tikitin takara kai tsaye batu ne na cikin gida da jam’iyyar za ta magance bisa ƙa’idojinta.
Ana son Abba ya koma jam'iyyar APC
A wani labarin, kun ji cewa jigo a APC, Alhaji Liadi Tella, ya tsoma baki a siyasar jihar Kano bayan ganawar da aka yi jiya tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
'Dan siyasar ya bukaci Gwamnan Kano da ya dauki abin da ya kira mataki na jarumtaka idan ya sauya sheka zuwa APC, ko da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bai amince ba
Shawarwarin na Liadi sun zo ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan makomar siyasar Kano da kuma yiwuwar sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf gabanin zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


