2027: Obasanjo Ya Ziyarci IBB yayin da Ya ke Neman Hada Kwankwaso, Obi
- Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kai ziyara ga tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a jihar Neja
- Ziyarar ta faru ne a daidai lokacin da ake kara jin rade-radi kan rawar da manyan tsofaffin shugabannin ke takawa gabanin zaben 2027
- Rahotanni sun danganta ganawar da hasashen shiryawa ko goyon bayan wasu dabarun siyasa da ke tattare da hadin gwiwar jam’iyyun adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Neja – Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kai wata ziyara ta musamman ga tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, a gidansa da ke Minna, babban birnin Jihar Neja.
Ziyarar ta gudana ne a ranar Litinin 19 ga Janairun 2026, inda Obasanjo ya isa Minna ta filin jirgin saman Ahmed Bola Tinubu kafin ya wuce kai tsaye gidan Babangida.

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya sake tayar da kura a fagen siyasar kasa, musamman ganin yadda ake ci gaba da rade-radin shirye-shiryen da ke tattare da zaben shugaban kasa na 2027.
Yadda Obasanjo ya ziyarci IBB
Majiyoyi sun bayyana cewa bayan isowarsa Minna, wasu jami'ai daga gidan gwamnatin Jihar Neja ne suka tarbi Obasanjo kafin ya nufi gidan tsohon shugaban mulkin sojan.
Leadership ta rahoto cewa ganawar ta kasance a bayan fage, inda Obasanjo da Babangida suka shafe kusan mintuna 30 suna tattaunawa ba tare da bayyana wa jama’a abin da suka tattauna ba.
Bayan kammala ganawar, Obasanjo ya koma filin jirgin sama inda ya bar Minna, lamarin da ya kara sanya al’umma cikin tambayoyi kan manufar ziyarar.
Hasashen kan hada Obi, Kwankwaso
Wata majiya ta shaida cewa ziyarar ba ta rasa alaka da muhimman batutuwan kasa da kuma shirye-shiryen zaben 2027 da ke kara daukar hankali.
A ‘yan kwanakin nan, ana ta danganta sunan Obasanjo da wasu dabarun siyasa da ake zargin suna nufin samar da tikitin hadin gwiwa tsakanin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.
Rahotanni sun ce ana hasashen Obi zai tsaya takarar shugaban kasa, yayin da Kwankwaso zai zama mataimakinsa a karkashin jam’iyyar ADC.

Source: UGC
Idan har hakan ta samu nasara, ana ganin hadin gwiwar za ta zama babbar barazana ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Wasu rahotannin sun kara da cewa akwai wani shiri na daban da zai bai wa Obi da Kwankwaso damar tsayawa takara a wata jam’iyya idan ba su samu tikitin ADC ba.
Dangantakar Babangida da Kwankwaso
Haka kuma, an rawaito cewa Ibrahim Babangida ya shawarci Rabiu Musa Kwankwaso da ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa ADC.
Masu lura da al’amuran siyasa na ganin wannan shawara a matsayin wani bangare na babbar dabarar siyasa da ake kokarin kulla wa gabanin zaben 2027.
Duk da haka, babu wata sanarwa a hukumance da ta fito daga Babangida ko Kwankwaso kan wadannan rahotanni da ake yadawa..
Kwankwaso ya yabi 'yan Kwankwasiyya

Kara karanta wannan
Harin tikitin ADC ya kara zafi, tsohon Minista ya ayyana shirin neman shugaban kasa a 2027
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yaba wa dakarun Kwankwasiyya masu kare akidar tafiyar a kafafen sadarwa.
A bayanin da ya yi, Rabiu Kwankwaso ya yaba musu, inda ya ce jajircewar da suke da hakuri na cikin tsarin tafiyar Kwankwasiyya.
Maganar shi na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin gwamna Abba Kabir Yusuf zai koma jam'iyyar APC mai mulki daga NNPP.
Asali: Legit.ng

