Zaben 2027: NNPP Ta Hango Makomarta a Kano bayan Ficewar Gwamna Abba

Zaben 2027: NNPP Ta Hango Makomarta a Kano bayan Ficewar Gwamna Abba

  • Alamu na ci gaba da nuna cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zainsauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC
  • Mai magana da yawun NNPP na kasa, Ladipo Johnson, ya makomar jam'iyyar a zaben shekarar 2027 idan Gwamna Abba ya koma APC
  • Ladipo Johnson ya bayyana cewa ko a zabubbukan shekarar 2019 da 2023, jam'iyyar NNPP ta samu nasara a Kano duk da cewa ba ta da gwamna mai ci

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Jam’iyyar NNPP ta yi tsokaci kan shirin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na sauya sheka zuwa APC.

Jam'iyyar NNPP ta bayyana kwarin gwiwar cewa za ta lashe zaben gwamnan jihar Kano a shekarar 2027, ko da kuwa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice zuwa APC.

NNPP ta ce za ta ci zabe a Kano a shekarar 2027
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Mai magana da yawun jam'iyyar NNPP na kasa, Ladipo Johnson, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Morning Brief' a ranar Talata, 19 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, an ji lokacin da Gwamna Abba zai zama 'dan APC a Kano

Alamu sun nuna Gwamna Abba zai koma APC

A ‘yan kwanakin nan, rahotanni sun karade gari cewa Gwamna Abba na shirin barin NNPP zuwa APC.

Ziyararsa ta baya-bayan nan ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta kara rura wutar jita-jitar shirin sauya sheka zuwa APC.

A ranar Litinin da ta gabata ne Gwamna Abba Yusuf ya kai ziyara ga Shugaba Tinubu, lamarin da ya sake tayar da rade-radin cewa yana dab da komawa APC.

NNPP ba ta fargaba a Kano

Sai dai, Ladipo Johnson, ya ce jam’iyyar ba ta damu da wannan yiwuwar sauya sheka ba, yana mai cewa NNPP ta riga ta kafa ingantaccen tsari a jihar Kano wanda zai ba ta damar cin zabe a 2027.

“Ina tunawa a 2019, ba mu da gwamna mai ci, ba mu da ‘yan majalisar dokoki ko kansiloli, amma mun yi imanin cewa mun lashe zaben Kano. Daga baya INEC ta ce zaben bai kammala ba, sannan Ganduje ya sake lashe zaben."

Kara karanta wannan

APC ta sace gwiwar gwamnonin da ke tururuwar sauya sheka gabanin zaben 2027

“Har a 2023 ma, irin wannan yanayin ne. Mun fafata da APC, kuma Abba Kabir Yusuf kansa ya san cewa ya lashe zaben."
"NNPP ce ta ci zabe, ta lashe mafi yawan kujeru, duk kuwa da cewa ba mu da jami’an gwamnati a wancan lokaci, ba kansiloli, ba kowa.”

- Ladipo Johnson

Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin komawa APC
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jawabi a wajen taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Meyasa NNPP ke samun nasara a Kano?

Ladipo Johnson ya kara da cewa jam’iyyar ta samu nasara ne bisa goyon bayan jama’a, ba tare da karfin mulki ba.

“Mun iya cin Kano, kuma da yardar Allah, a 2027 ma haka zai kasance, ko yana tare da mu ko kuma ya bar mu. Wannan ba girman kai ba ne, siyasa ce kawai, kuma ina da yakinin za mu sake cin Kano."

- Ladipo Johnson

Tinubu ya sharewa Abba hanyar shiga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya tattauna muhimman batutuwa tare da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Majiyoyi da dama da ke da masaniya kan ganawar sun bayyana cewa, tattaunawar ta warware muhimman matsalolin siyasa da suka dakatar da shirin sauya shekar gwamnan a baya.

Sun bayyana cewa Shugaba Tinubu ya sharewa Gwamna Abba fagen shiga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya a hukumance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng